Hukumar kwastam sun kwace haramtattun kayayyaki na kimanin N50m

Hukumar kwastam sun kwace haramtattun kayayyaki na kimanin N50m

- Hukumar kwastam ta kama haramtattun kayayyaki

- An tattaro cewa farashin kayayyakin da aka kama sun kai kimanin naira miliyan 50

- Jami'an sun kama kayayyakin ne a yankin Zone 'D'

Hukumar hana fasa kwabri ta kama motoci biyar shake da haramtattun kayayyaki wadda suka kai kimanin naira miliyan 50.2.

Shugaban hukumar na Zone ‘D’, wadda suka hada da jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Bauchi, Gombe, Plateau, Benue da Nasarawa, Peters Olugboyega, ya bayyana hakan a ranar Litinin, 3 ga watan Satumba a wani taron manema labarai a hedkwatar hukumar dake Bauchi.

Jami’an hukumar ne suka yi kamun a sintirin da suka yi tsakanin ranar 31 ga watan Agusta da 3 gaa watan Satumba.

Olugboyega ya kara da cewa kayayyakin sun sabama ka’idar abubuwan da aka amince da sufurinsu kuma ya sabama sashi na 4 na hukumar kwastam din.

Yace kudaden da aka biya akan motar da kayayyakin sun kama N32,282,000.

Hukumar kwastam sun kwace haramtattun kayayyaki na kimanin N50m
Hukumar kwastam sun kwace haramtattun kayayyaki na kimanin N50m
Asali: Depositphotos

Shugaban kwastam din yace an kama wani mota kirar Mercedes Benz 911, mai lamba XG 433 RSH, a ranar 1 ga watan Satumba, 2018, da misalin karfe 7:49 na yamma a hanyar Bauchi-Jos dauke buhuhunan shinkafa yar waje 300 nade a buhuhunan BUA.

KU KARANTA KUMA: Wasu Magoya bayan Buhari sun maidawa wani mutumi kudin da ya kashe wajen ganin APC tayi nasara a 2015

Yace kudaden motar da kayayyakin ya kama N9,720,000.

Olugboyega ya cigaba da cewa akwai motocin J5 uku dauke da lamba, NSR 374 TRN; TRN 162 AU; da JJN 108 XP, dauke da kullin gwanjon kaya 90 da aka kama a hanyar Bauchi-Kano da misalin karfe 4:30 na safiyar ranar 3 ga watan Satumba.

Yace kudin kayayyakin da motocin ya kama N8,235,000.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel