2019: Ya zama dole PDP su hada kai don kayar da Buhari – Cewar Fayose yayinda ya tarbi Atiku

2019: Ya zama dole PDP su hada kai don kayar da Buhari – Cewar Fayose yayinda ya tarbi Atiku

Dan takaran kujerar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar yayi tattaki zuwa jihar Ekiti domin neman goyon bayan tawagar jihar a babban taron jam’iyyar da za’a gudanar cewa yana na shiri na musamman don ci gaban Najeriya.

Da yake tarban dan takaran shugaban kasar a Ekiti, gwamnan jihar, Ayodele Fayose ya bayyana cewa ya zama dole yan PDP su hada kai domin ganin sun kwace mulki daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa Gwamna Fayose yayi kira ga hadin kan mambobin jam’iyyar cewa Atiku na da duk abunda ake bukata wajen zama shugaban kasa.

2019: Ya zama dole PDP su hada kai don kayar da Buhari – Cewar Fayose yayinda ya tarbi Atiku
2019: Ya zama dole PDP su hada kai don kayar da Buhari – Cewar Fayose yayinda ya tarbi Atiku
Asali: UGC

Yace babban kalubale da jam’iyyar PDP zata iya fuskanta shine kin yin aiki a matsayin yan uwan juna.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Har yanzu ina a PDP - Shekarau

A halin da ake ciki Atiku yace zarge-zargen rashawa da ake yi masa karya ne ba gaskiya bane.

Ya kasance mataimakin shugaban kasa a karkashin gwamnatin Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007.

Atiku ya raba gari da ubangidansa jim kadan bayan zaben 2003 wadda PDP tayi nasara. Sai daga baya aka zarge shi da hannu a rashawa wadda majalisar dattawa ya bincike shi akai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel