Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Rundunar yan sanda a jihar Gombe sun samo dala 4,000 (kimanin naira miliyan 1.3) daga hannun wani matashin yaro dan shekara 19 bayan sun kama shi a garin Pindiga dake karamar hukumar Akko dake jihar, kakakin rundunar ta tabbatar.
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata a yanzu, Rabiu Musa ya kaddamar da ra’ayinsa na tsayawa takara a zaben 2019 karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Kwankwaso ya bayyana kudirin nasa ne a wajen wani taro.
Bayan kammaluwar aikin hajji, Alhazai sun fara komawa kasashensu na haihuwa. Dama dai da zaran an kammala aikin hajji hankalin ko wani Alhaji da Hajiya kan koma gida, domin ganin sun isa ga yan uwansu bayan wasu makonni ana ibadah
Firai ministar Birtaniya Theresa May za ta ziyarci Najeriya a wannan makon da muke ciki. Bisa ga rubutun da aka wallafa a shafin twittar babban kwamishinan Birtaniya a Najeriya, Paul Arkwight, @paulTarkwight yace yana farin ciki.
A ranar Litinin, 27 ga watan Agusta, gwamnatin tarayya ta fitar da jerin ayyukan ginin tituna da gadoji da ta ce tana yi a kudu maso gabashin Najeriya. Ministan bayanai da al'addu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana hakan.
Tun bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi takawar mita 800 daga masallaci zuwa gidansa a lokacin bkin babban Sallah, mutane tare day an siyasa na ta tofa albarkatun bakunansu. Wasu yan siyasa na ganin zasu iya fiye da hakan
Gwamnan Jihar Barno, Kashim Shettima, ya bayyna cewa ba shi masaniyar wanda zai canje shi, a matsayin gwamnan jihar bayan wa’adin sa ya kare a watan Mayu na 2019 mai zuwa. Ya ce ya bar wa Allah ya zabar wa al’ummar jihar gwamna.
Shugaban kungiyar matasan Arewa kan zaman lafiya da tsaro, Salisu Magaji ya shawarci kungiyar Miyetti Allah da ta mayar da hankali wajen taimakawa domin kawo karshen kashe-kashe maimakon sanya baki a harkokin siyasa.
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ba wai don an magance rikicinsa da shugabancin jam’iyyar na jihar Kaduna ba ne yasa shi ci gaba da kasancewa a jam’iyyar ba, sai dai saboda sanya bakin da Shugaba Buhari da Oshiomhole suka yi.
Aisha Musa
Samu kari