APC Ta Yi babban Rashi: Tsohon Sanata kuma Jigonta Ya Yi Bankwana da Duniya
- Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi alhinin rasuwar fitaccen lauya kuma tsohon Sanata mai wakiltar Ekiti ta Kudu
- Oyebanji ya bayyana cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen dawo da mulkin masu ra'ayin ci gaba a Ekiti tare da bayar da gudunmawar shari'a
- Gwamnan ya ce za a tuna da Adeniyi saboda hidimarsa a Majalisar Dattawa, fannin shari'a da kuma gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Ekiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ado-Ekiti, Ekiti - Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi jimamin rasuwar fitaccen lauya kuma jagoran APC a jihar.
Oyebanji ya bayyana rasuwar Sanata Anthony Ademuyiwa Adeniyi, SAN a matsayin abin takaici.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Yinka Oyebode, ya fitar, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Kano ta yi zarra, ta fi dukkan jihohin Najeriya sababbin masu rijistar katin zaɓe
Tsohon sanata ya mutu a Ekiti
Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ranar Laraba 24 ga watan Yunin 2026 yana da shekara 75 da haihuwa a duniya.
Adeniyi ya wakilci mazabar Sanatan Ekiti ta Kudu a Majalisar Dattawa tsakanin shekarun 2011 da 2015.
Gwamna Oyebanji ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga Ekiti da Najeriya, ya ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen dawo da mulkin masu ra'ayin ci gaba a Ekiti wanda har yanzu ke da tasiri.
Ya ce tarihin dawo da wa'adin masu ra'ayin ci gaba wanda ya kai ga rantsar da tsohon gwamna Kayode Fayemi a shekarar 2010 ba zai cika ba.
Oyebanji ya bayyana cewa marigayin ya wakilci al'ummar Ekiti ta Kudu da ƙwazo a Majalisar Dattawa. Ya ce ya jagoranci batutuwan gyaran kundin tsarin mulki da zabe.
Haka kuma, ya yi fafutuka wajen tabbatar da 'yancin bangaren shari'a, inganta ayyukan kamfanonin sadarwa da kuma jawo hannun jari zuwa tattalin arzikin Najeriya.

Source: Original
Gudunmawar da marigayi sanatan ya bayar
Gwamnan ya yaba da rawar da Adeniyi ya taka a kungiyar lauyoyi ta NBA, ya taba zama shugaban reshen Akure tsakanin shekarun 1990 da 1992.
Ya kuma yabawa aikin da marigayin ya yi a matsayin shugaban hukumar gudanarwar tsohon bankin Omega, inda bankin ya samu fadada ayyuka da karuwar jarin kasuwanci.
Oyebanji ya ce za a ci gaba da tuna da mamacin ɗan asalin Ikere Ekiti saboda kyawawan ayyuka da gado mai ɗorewa da ya bari ga al'umma, cewar Daily Post.
Ya kara da cewa:
"Mun rasa dattijo nagari, fitaccen lauya da kuma ɗa na gari daga Ekiti. Ya rayu rayuwa mai cike da hidima."
Gwamnan ya yi addu'ar Allah Ya jikansa da rahama tare da bai wa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi da suka yi.
Babban Sarki ya rasu a Najeriya
A wani labarin, an ji cewa an tabbatar da rasuwar fitaccen basarake a Najeriya yana da shekaru 82 bayan fama da jinya na wani lokaci.
Alara na Aramoko Ekiti, Oba Olu Adegoke Adeyemi, ya rasu bayan ya yi shugabanci mai cike da hikima da nasarori.
Iyalansa sun bayyana mulkinsa a matsayin lokaci da ya kawo hadin kai, ci gaban al’adu, zaman lafiya da inganta rayuwar matasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

