Ambaliyar ruwa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 9 a jihar Kano

Ambaliyar ruwa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 9 a jihar Kano

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Kano (SERERA) Ali Bashir ya bayyana cewa mutane tara sun rasa rayukan su sannan wasu biyar sun ji rauni a dalilin ruwa da akayi kamar da bakin kwarya a jihar.

Bashir ya bayyana hakan ne ranar Laraba da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kano.

Akalla kananan hukumomi 9 ne suka yi fama da ta’adin da ambaliyar ruwan ya shafa.

Ambaliyar ruwa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 9 a jihar Kano
Ambaliyar ruwa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 9 a jihar Kano
Asali: Depositphotos

“Mutane sama da 4,475 a kananan hukumomi tara dake jihar ya shafa sannan mutane biyar sun rasa rayukan su a kauyen Rimin Gado, uku a Gabasawa da kuma daya a garin Getso kuma duk a karamar hukumar Gwarzo.”

Ya kara da cewa da zaran hukumar ta kammala gudanar da bincike za ta gabatar da sakamakon binciken ga gwamnatin jihar.

A wani lamari makamncin haka, an tattaro cewa wata uwa mai goyo da danta tare da wasu mutane sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a karamar hukumar Kontogora dake jihar Niger a ranar Asabar, hukumar bayar da agajin gaggawa na jiha (NSEMA) ya tabbatar a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: PDP ta tabbatar da tattaunawa da gwamnonin APC 6 da yan majalisa 27

An tattaro cewa matar Bafulatana ce goye da danta a bayanta, darakta janar na NSEMA, Malam Ahmed Ibrahim Inga ya fadi.

Yace daga cikin wadanda suka rasa ransu akwai yarinya yar shekara hudu, Ummi Khaira wacce ta rasa ranta bayan ginin laka ya rufto mata a inda ta fake tare da sauran yara yankin Rigara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel