Kanin Dankwambo da na hannun damansa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC

Kanin Dankwambo da na hannun damansa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Kanin Gwamna Dankwambo ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC

- Buhari Mohammad Dankwambo ya tabbatar da hakan ga manema labarai

- Haka zalika na hannun daman gwamnan, Auwal Abdullahi Gafakan Akko ma ya bar PDP

Kudirin takaran shugabacin kasa na Gwamnan jihar Gombe Ibraim Hassan Dankwambo na iya samun cikas sakamakon shirin sauya sheka a kaninsa, Buhari Mohammed Dankwambo wadda aka fisani da BHD da wani babban na hannun daman gwamnan, Auwal Abdullahi Gafakan Akko ke shirin yi zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Yayinda yake tabbatar da lamarin ga ‘yan jarida da manema labarai a Gombe a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba, Buhari Dankwambo yace ya kammala duk wani shiri na sauya sheka zuwa APC inda ya bayyana cewar abunda ya kawo jinkirin bayyanawa jama’a shine bukatar da wasu masu ruwa da tsaki a APC suka nema na cewa ya zama dole ayi babban taro domin zai koma jam’iyyar ne dubbin magogaya baya.

Kanin Dankwambo, da na hannun damansa sauya sheka daga PDP zuwa APC
Kanin Dankwambo, da na hannun damansa sauya sheka daga PDP zuwa APC
Asali: Twitter

Wata majiya ta kusa da yan’uwan gwamnan ta bayyana cewa Buhari ya taka muhimmin rfawar gani waje marawa yayan nasa baya ta hayar kashe makudan kudade wajen neman goyon bayan mutane a fadin jihar lokacin da Dankwabo ke neman tazarce a 2015 wadda akayi zargin cewa bayan yayan nasa ya yi nasara sai ya yi watsi dashi.

A halin yanzu, Auwal Abdullahi Gafakan Akko wani babban magoyin bayan Gwamna Hassan Dankwambo a karamar hukumar Akko dake jihar ma ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC) a jihar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rundunar soji sun kashe yan ta’adda, sun samo dabbobi 147 da aka sace a Borno

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Jam’iyyar All Progressives Congress ta bukaci yan takaranta dake neman kujerun majalisar dokoki na jiha, wadanda basu siya takardan takaransu ba a jihohinsu da su zo sakatariyar jam’iyyar.

Jam’iyyar a wata sanarwa da ta fitar ta mukaddashin sakaaren labaranta na kasa, Yekini Nabena, yace jam’iyyar ta samu korafi daga wasu yan tara kujerun majalisar jiha cewa basu samu damar mallakar fam din ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel