Zargin Bata Suna: Fasto Ayodele Ya Fayyace komai a Martani ga Barazanar Kwankwaso

Zargin Bata Suna: Fasto Ayodele Ya Fayyace komai a Martani ga Barazanar Kwankwaso

  • Fasto Elijah Ayodele ya yi martani bayan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya shirya shigar da shi kara kan zargin bata suna
  • Ayodele ya musanta zargin bata suna da Rabiu Kwankwaso ya yi masa, yana mai cewa kalamansa na wahayi ne ba suka ba ne ga kowa
  • Kwankwaso ya yi barazanar shigar da karar neman diyyar Naira biliyan 10, bayan zargin cewa Ayodele ya yi kalaman da suka shafi dangantakarsa da Peter Obi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Jagoran cocin INRI Evangelical Spiritual Church da ke Lagos, Fasto Elijah Ayodele, ya yi magana kan barazanar Rabi'u Kwankwaso.

Faston ya musanta zargin bata suna da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi masa.

Fasto Ayodele ya yi martani kan barazanar Kwankwaso
Fasto Elijah Ayodele da Sanata Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Primate Elijah Babatunde Ayodele, Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

Da yake mayar da martani ta bakin mai taimaka masa wajen yada labarai, Osho Oluwatosin, Ayodele ya ce bai taba nufin bata sunan Kwankwaso ba, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Zargin bata suna: Kwankwaso ya yi barazanar kai malamin addini kotu, zai nemi N10bn

Zargin da Kwankwaso ke yi wa Ayodele

A cikin wata wasika daga lauyan Kwankwaso, an zargi Ayodele da yada wani wa’azi kai tsaye wanda a ciki ya yi tambaya kan sahihancin gaskiyar Kwankwaso da Peter Obi.

Lamarin ya biyo bayan barazanar da Kwankwaso ya yi na shigar da karar neman diyyar Naira biliyan 10 kan abin da ya bayyana a matsayin kalaman bata suna.

An bayyana Peter Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, kuma kalaman da aka danganta wa malamin sun haifar da ce-ce-ku-ce.

Martanin Ayodele ga Sanata Kwankwaso

Ya bayyana cewa abin da ya fada wahayi ne kawai kuma ba wani suka kai tsaye ba ne ga Kwankwaso ko wani dan siyasa.

Ayodele ya ce sakonninsa suna fitowa ne daga Ubangiji kuma ba su da alaka da wata matsala ko sabani da tsohon gwamnan Kano.

Ya ce:

“Na fahimci cewa Rabiu Kwankwaso ya yi zargin cewa na yi masa kalamai marasa kyau a cikin sabon bidiyo da na yi.”

Kara karanta wannan

Kocin kungiyar kwallon kafa ya sha da kyar kan zargin satar mazakuta

Fasto ya wanke kansa kan zargin bata sunan Kwankwaso
Fitaccen Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele. Hoto: Primate Elijah Ayodele.
Source: Facebook

Manufar abin da Fasto ke yi

Faston ya kara da cewa manufar wahayinsa ba ta taba kasancewa ta bata suna, cin mutunci ko kai hari ga mutuncin wani mutum ba.

A cewarsa, yana magana ne bisa abin da ya karba daga Ubangiji kuma ba ya yin hakan saboda wata manufa ta kashin kai.

Malamin ya ce bai taba haduwa da Kwankwaso ba kuma babu wata matsala ta kashin kai tsakaninsu da za ta sa ya kai masa hari, cewar TheCable.

Ya bayyana cewa yana girmama Kwankwaso kamar yadda yake girmama sauran mutane, kuma wahayi da yake yi ba su dogara da son rai ba.

Ayodele ya nuna takaicinsa kan yadda aka juya kalamansa a matsayin yunkurin bata sunan tsohon gwamnan maimakon sakon wahayi.

Ya ce da an nemi karin bayani daga gare shi tun farko, da ya bayyana abin da yake nufi kuma da an fahimci cewa bai yi nufin bata suna ba.

Kara karanta wannan

Rarara ya zargi Kwankwaso da jefa Najeriya cikin halin kunci, ya kawo dalili

Fasto ya fadi masu daukar nauyin ta'addanci

An ji cewa Fasto Elijah Ayodele ya yi zargin cewa akwai masu hannu a daukar nauyin ta'addanci a cikin jami'an gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Fitaccen malamin cocin ya gargadi gwamnatin tarayya cewa ya kamata ta tashi tsaye domin kawo karshen duk wata barazana ta tsaro.

Ayodele, wanda ya shahara wajen hasashen abin da zai faru, ya bayyana ‘yan ta’adda a matsayin makiyan kasa masu taurin kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.