An gurgunta Boko Haram, babu wasu yan ta’adda dake sake kafuwa a arewa maso gabas - Buratai
Shugaban hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai a ranar Talata, 3 ga watan Satumba ya sake bayyana cewa an gurgunta yan ta’addan Boko Haram sannan kuma cewa babu yan ta’adda dake sake kafuwa a Arewa maso gabashin kasar kamar yadda ake rade-radi.
Buratai, wadda yayi Magana a Jaji wajen yaye runduna 55 na musamman yace “a rayuwa, dole mutun ya fuskanci wasu kalubale.”
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa a yan kwanakin da suka gabata, akwai rahoton labarai dake cewa yan ta’adda sun kai hari ga sojoji a yankin arewa maso gabas inda akayi ikirarin cewa an kashe wasu sojoji.
Sai dai rundunar sojin ta karyata harin da kuma cewar ta rasa jami’anta.

Asali: Depositphotos
Buratai yaje Jaji netare da rakiyan babban hafsan sojin Afrika ta Kudu, Laftanar Janar Lindile Yam wadda ya kawo ziyara kasar.
KU KARANTA KUMA: Dubi Ronke Ajayi wacce ta sha alwashin siyar da dukkanin abunda ta mallaka don siyawa Buhari fam din takara
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu wani yanki a kasar dake karkashin ikon yan ta’addan Boko Haram a yanzu.
Ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 2 ga watan Satumba, a Beijing, kasar China yayinda yake bayyana wasu nasarori da gwamnatinsa ta samu a lokacin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya mazauna kasar.
Shugaban kasar ya danganta nasarorin ga ayyukan da hukumomin tsaro suka gudanar wajen yakar ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng