Wata 'Yar Sanda Ta Jefa Kanta a Shari'ar N300m a Abuja, Kotu Ta Sa a Kamo Ta
- Kotu ta bada umarnin kama jami’ar ‘yan sanda Edith Erhunwuse saboda ci gaba da kin bayyana a kotu kan shari’ar da ake zarginta da hannu
- Ana zargin jami’ar da hannu wajen korar mutane da karfi tare da lalata kadarori da darajarsu ta kai N300m, lamarin da ya kai ga gurfanar da ita
- Alkaliya Samira Bature ta umurci dukkan hukumomin tsaro su kamo Erhunwuse, bayan ta ce rashin halartarta ya jawo tsaiko ga shari’ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Babbar kotun babban birnin tarayya ta bayar da umarnin kama wata jami’ar ‘yan sanda, Edith Erhunwuse, saboda ci gaba da kin bayyana a gabanta kan shari’ar da ake zarginta da hannu a ciki.
Alkaliya Samira Bature ce ta bayar da umarnin a ranar Alhamis yayin zaman shari’ar mai lamba FCT/HC/CR/222/2023.

Source: Getty Images
Zarge-zargen da ake yi wa 'yar sandan
Shari’ar ta shafi zargin korar mutane ba bisa ka’ida ba da kuma lalata kadarori da ake cewa darajarsu ta kai Naira miliyan 300, a cewar rahoton The Cable.
Lauyar gwamnati, Aderonke Imana, ta nemi kotun ta sake bayar da sammacin kama Erhunwuse bayan ta bayyana cewa an taba bayar da irin wannan umarni a baya.
Imana ta shaida wa kotun cewa an riga an aika wasiku ga kwamishinan ‘yan sanda na Abuja kan umarnin da aka bayar a baya, amma har yanzu jami’ar ba ta bayyana a kotu ba.
Ta ce duk da wani umarni na Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Erhunwuse ta ci gaba da kauce wa zaman kotu.
A cewarta, jami’ar ta yi watsi da hanyoyin shari'a sama da shekara guda, yayin da sauran wadanda ake kara ke ci gaba da halartar zaman kotu.
Kotu ta sake bayar da sammacin kama ta
Da take yanke hukunci, Mai shari'a Samira Bature ta ce babu wani ci gaba da aka samu tun bayan bayar da umarnin kama na farko kimanin watanni biyu da suka gabata.
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa Samira Bature ta kuma bayyana cewa hutun kotuna da ke gabatowa na iya kara jinkirta ci gaban shari’ar.
Alkaliyar ta amince da bukatar lauyan gwamnati tare da umartar dukkan hukumomin tsaro su kama Erhunwuse a duk inda aka same ta.
Ta ce:
“Wannan kotu ta bayar da sammacin kama wanda ake kara na uku ga dukkan hukumomin tsaro domin a kama ta a duk inda aka same ta saboda rashin biyayya da rashin mutunta wannan kotu.”

Source: UGC
An dage shari’ar zuwa watan Satumba
Sai dai kotun ta bukaci bangarorin da ke cikin shari’ar su ci gaba da kokarin cimma matsaya a wajen kotu. An dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 29 ga Satumba.
A zaman kotun, A.S. Usman ya wakilci wanda ake kara na farko, yayin da A.K. Musa ya rike matsayin mai sa ido ga mai karar. Victor Giwa kuma ya wakilci kansa a matsayin wanda ake kara na biyu.
Bidiyon d'an sanda yana shan giya
A wani labari, mun ruwaito cewa, wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya ya nuna wani jami’in ‘yan sanda yana shan abin da ake zargi barasa ce yayin da yake aiki.
Jama’a sun yi Allah-wadai da lamarin tare da neman a dauki mataki idan aka tabbatar da cewa jami’in d'an sanda ya aikata laifi.
Bayan bullar bidiyon da ce-ce-ku-cen jama'a, rundunar ‘yan sanda ta ce ta fara bincike domin gano jami’in da wurin da abin ya faru.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


