2019: Dalilin da yasa nake son zama Gwamnan Zamfara – Dan majalisa Jaji

2019: Dalilin da yasa nake son zama Gwamnan Zamfara – Dan majalisa Jaji

- Wani dan majalisar wakilai mai wakiltan Kaura-Namoda/Birnin-Magaji dake jihar Zamfara ya shiga tseren kujerar gwamnan jihar

- Aminu Sani-Jaji (APC Zamfara) a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba ya yanki fam din takara

- Yace yana son kakkabe ta’adin gwamnatocin baya da sabonta jihar

Wani dan majalisar wakilai mai wakiltan Kaura-Namoda/Birnin-Magaji dake jihar Zamfara a majalisar wakilan kasar, Aminu Sani-Jaji (APC Zamfara) a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba ya shiga tseren neman kujerar gwamna domin “kakkabe ta’adin gwamnatocin baya da sabonta Zamfara.”

Jaji wadda ya bada Karin haske a Abuja bayan ya mallaki fam din takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya soki kokarin bin yanki da masu ruwa tsaki na jam’iyyar a jihar ke kokarin yi cewa hakan tursasawa ne kuma baya bisa ka’ida.

2019: Dalilin da yasa nake son zama Gwamnan Zamfara – Dan majalisa Jaji
2019: Dalilin da yasa nake son zama Gwamnan Zamfara – Dan majalisa Jaji
Asali: UGC

Dan majalisan ya bayyana fam din takaran a matsayin matakin kawo cigaba a Zamfara da kuma hawa da ita tudun tsira, musamman ta fannin ilimi, tsaro da kayayyakin more rayuwa.

A cewarsa shiga tseren zaben gwamna ya nuna kaifin siyasan sa da kuma karyata makiyan damokradiyya, yayinda ya sha alwashin marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a 2019.

KU KARANTA KUMA: Saraki ya caccaki kakakin jam’iyyar APC, ya kalubalance shi da suyi muhawara

Ya bayyana cewa: “Kafin na mallaki wannan fam din, sun yi kokarin ganin sakatariyar bata saida mun da fam din ba saboda sun san cewa ina daga cikin masu addu’an Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo a 2019.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel