Gwamnatin tarayya ta nada sabon shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri

Gwamnatin tarayya ta nada sabon shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri

- Gwamnatin tarayya ta nada Ahmed Ahidjo a matsayin babban daraktan likitoci na asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri

- Boade Akinola, daraktan harkokin labarai na ma’aikatar lafiya ne ya sanar da nadin

- Ministan lafiya, Isaac Adewole ya tunatar da Ahidjo muhimmancin matsayin da ya hau

A ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba, gwamnatin tarayya ta amince da nadin Ahmed Ahidjo a matsayin babban daraktan likitoci na asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Boade Akinola, daraktan harkokin labarai na ma’aikatar lafiya ne ya sanar da nadin a cikin wata sanarwa a Abuja.

Gwamnatin tarayya ta nada sabon shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri
Gwamnatin tarayya ta nada sabon shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri
Asali: Depositphotos

A nashi bangaren ministan lafiya, Isaac Adewole ya tunatar da Ahidjo muhimmancin matsayin da ya hau.

Adewole ya kuma sanar da shi hakokkin mutane akan ma’aikatar lafiya inda ya bukaci sabon shugaban da yayi aikin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada shi da aminci.

KU KARANTA KUMA: Idan makamai kuke nema ku tafi Sambisa – Shehu Sani ga yan sanda

Nadin Ahidjo zai shafe shekaru uku ne farawa daga ranar 3 ga watan Satumba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel