Dalilina na kin sa wa kudirin zabe hannu - Buhari
- Shugaba Buhari ya bayyana hujjarsa na kin sanya hannu a dokar zabe
- Yace akwai wasu batutuwa da ba'a warwareba kafin majalisa ta gabatar masa da kudirin
- Hadimin shugaban kasar kan lamuran majalisar ne ya bayyana hakan
Shugaba Muhammadu Buhari ya daura alhakin kin sanya hannunsa a kudirin gyara zabe kan wasu “hardaddun batutuwa” da ba a warware ba a lokacin da majalisa ta aike masa da kudirin.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman akan lamuran majalisar dattawa, Ita Enag ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a babban birnin tarayya, Abuja.
Ya ce tuni shugaban kasar ya sanar da majalisar dokokin kasar hakan tun a ranar 30 ga watan Agusta.

Asali: Facebook
Buhari ya ki sanya hannu ne kan kudirin dokar zabe, saboda har yanzu akwai sauran lauje a cikin nadin, domin akwai sauran batutuwan da majalisa ba ta tabo ba a lokacin da ka gabatar da kudirin.
KU KARANTA KUMA: 2019: APC Sokoto sun tsayar da Shugaba Buhari
Ya ce akwai batu na abinda Doka ta Sashe na 87 (14) na dokar zabe ya tanada, wanda ya yi magana kan takamaimen ranakun da za a gudanar da zabukan fidda-gwani na jam’iyyun siyasa.
Ya ce Majalisar ta yi gaggawar aika wa Shugaban Kasa kudirin dokar gyaran ranakun zabe, ba tare da yin la’akari da yinn gyara a sashen doka na 31, 34 da kuma na 85 ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng