Gwamnatin Jihar Niger ta kashe N2.6bn wajen biyan hakkin ‘yan fansho 1,599

Gwamnatin Jihar Niger ta kashe N2.6bn wajen biyan hakkin ‘yan fansho 1,599

- Gwamnatin jihar Niger ta kashe naira nbiliyan 2.6 wajen biyan yan fansho

- Yan fansho 1,599 ne suka amfana daga matakin ma'aikatan kananan hukumomi zuwa na jiha

- Anyi biyan kudaden ne a rukun daban-daban

Gwamnatin Jihar Niger ta sanar da cewa ta fitar da naira biliyan 2.6 domin ta biya hakkin kudaden ‘yan fansho har su 1,599 daga cikin ma’aikatan kananan hukumomi da na jiha.

Darakta Janar na Hukumar Fansho, Usman Muhammad ne ya sanar da hakan ga manema labarai a jiya Talata, 4 ga watan Satumba a garin Minna, babban birnin jihar Niger.

Ya kara da cewa an biya adadin kudin naira biliyan 1 ga ma’aikatan gwamnatin jiha sai kuma naira biliyan 1.5 ga ma’aikatan kananan hukumomi.

Gwamnatin Jihar Niger ta kashe naira biliyan 2.6 wajen biyan hakkin ‘yan fansho 1,599
Gwamnatin Jihar Niger ta kashe naira biliyan 2.6 wajen biyan hakkin ‘yan fansho 1,599
Asali: UGC

Daga nan sai ya ce jimlar wadanda suka ci moriyar biyan na su hakkin sun kai mutum 1,599.

KU KARATA KUMA: 2019: APC Sokoto sun tsayar da Shugaba Buhari

Muhammad ya ce ma’aikatan gwamnatin jiha su 456 ne yayin da na kananan hukumomi kuma su 1,14.

Ya ce an yi biyan kudaden fansho din aji daban-daban har sau hudu, amma cikon na biyar daga ma’aikatann kananan hukumomin ba a kai ga damka musu na su kudaden ba tukunna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel