Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Wata kotun Majistare dake garin Minna, babban birnin Jihar Niger, ta bada umarnin a garkame wani magidanci a kurkuku, sakamakon zargin sa da ake yi da hannun a mutuwar matar sa. Sai dai kuma wanda ake zargin yaki amsa laifin.
Rahotanni dake zuwa mana sun nunacewa wani Jirgin bincike na dakarun sojin Rasha ya bace a tekun Mediterranean dauke da sojojin kasar su 14. Jirgin ya bata ne a hare-hare da Isra'ila ta kai ta sama akan asar Syria.
Gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Aminu Tambuwal, yace zai karbi sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda za’a gudanar a watan Oktoba.
Fasto Amos Olugbenga na cocin Christ Kingdom, Ilorin yayi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su sanya dokar da zai yi duba ga shigar banga a kasar. Olugbenga yayi kiran ne a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya.
Babban hukumar kasar Birtaniya a Najeriya tace ziyarar da Theresa May, Fiaye Ministar Birtaniya ta kawo kwanan nan, ba yana nufin tsayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari kowani dan takara bane a zaben 2019 mai zuwa.
Wasu garuruwa a yankin Plateau ta arewa karkashin jagorancin kungiyar Berom Educational and Cultural Organization (BECO) sun bayyana cewa sun rasa kimanin mutane 300 wadanda mafi akasarinsu mata ne da yara cikin watanni hudu.
Wani babban limamin cocin Anglican, Steohen Oni, yace kasar nan na bukatar matashi kuma mutun mai hangen nesa da zai zamo shugaban kasar na gaba sannan kuma ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya ajiye kudirinsa na tazarce
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya mayar da fam dinsa na ra’ayin takarar kujerar gwamna a zaben 2019 sakatariyar All Progressives Congress (APC) dake Abuja. Ya kuma goyi bayan zaben fidda gwani na kato-bayan-kato.
Wani mai maganin gargajiya, Ganiyu Idowu mai shekaru 62 ya fadi gaskiyar cewa ya hada kai da wani Alfa Bamigbola Edun domin suyi kudin asiri da mai koyon aiki a wajensa. A jiya ne rundunar yan sandan jihar Ogun suka gurfanar da su
Aisha Musa
Samu kari