Na hada kai da wani malamin tsubbu don muyi kudi da mai koyon aiki a wurina – Mai magani

Na hada kai da wani malamin tsubbu don muyi kudi da mai koyon aiki a wurina – Mai magani

Wani mai maganin gargajiya, Ganiyu Idowu mai shekaru 62 ya fadi gaskiyar cewa ya hada kai da wani Alfa Bamigbola Edun domin suyi kudin asiri da mai koyon aiki a wajensa.

A jiya ne rundunar yan sandan jihar Ogun suka grfanar da Idowu, Edun da wani Mathew Odunewu a hedkwatar rundunar, Eleweran, Abeokut bisa zargin garkuwa da Ganiyu Akanni don yin kudin asiri.

Idowu, wani mai maganin gargajiya ya fadama manema labarai cewa Edun ya nemi ya kawo wani mutun domin yi masa kudin asiri da zai kai kimanin naira miliyan 11.

Na hada kai da wani malamin tsubbu don muyi kudi da mai koyon aiki a wurina – Mai magani
Na hada kai da wani malamin tsubbu don muyi kudi da mai koyon aiki a wurina – Mai magani
Asali: Twitter

Amma Edun ya karyata zargin, cewa shi dai kawai ya koyar da mai maganin ne wani hikima akan aikinsu. “ban san komai akan abunda yake fadi ba,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Sai na kwace tikitin APC daga hannun Badaru domin ya sauka daga hanyar chanji – Ubale Yusuf

Kwamishinan yan sandan jihar Ogun, Ahmed Iliyasu yace an kama masu laifin ne a kogin Ogun a kokarinsu na yanyanka wanda abun ya shafa don kudi.

“Da ake bincike, sun fadi gaskiyar cewa ledojin da aka same shi da su zasuyi amfani dashi ne wajen kwasan kasonsu na sassan jikin yaron bayan sun kashe shi,” inji Iliyasu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel