An kashe mutane 300 a garuruwan Plateau

An kashe mutane 300 a garuruwan Plateau

- Akalla mutane 300 aka rahoto cewa an kashe a jihar Plateau a watanni uku da rabid a suka gabata

- Wasu garuruwa a yankin Plateau ta arewa, karkashin kungiyar BECO suka bayyana hakan a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba

- Kungiyar ta kuma yi kira ga kasashen waje da su kawo masu agaji

Wasu garuruwa a yankin Plateau ta arewa karkashin jagorancin kungiyar Berom Educational and Cultural Organization (BECO) sun bayyana cewa sun rasa kimanin mutane 300 wadanda mafi akasarinsu mata ne da yara cikin watanni hudu da suka gabata.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba sun roki kasashen waje das u sanya baki wajen kawo karshen hre-haren a garuruwansu.

An kashe mutane 300 a garuruwan Plateau
An kashe mutane 300 a garuruwan Plateau
Asali: Depositphotos

Sun yi korafin cewa mace-mace ya afku ne tsakanin watan Yuni zuwa Satumba a kananan hukumomin Barkin-Ladi da Riyom.

A wata sanarwa daga babbar sakatariyar BECO Da Davou Choji; Shugaban BEWDA, Ngo Florence Jambol, da shugaban BYM Choji Chuwang, wanda aka sanar a Jos, sun bayyana cewa suna neman taimako daga kasashen waje don ceto su daga shafewa.

KU KARANTA KUMA: Dan kasuwa ya kawo cikas a hukuncin APC kan Buhari, ya shiga takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyya mai mulki

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa mutane uku ne suka mutu sanadiyar hatsari bayan fadiwar mota mai kirar Toyota Land Cruiser Prado cikin rafin Abarho a Okuokoko/Agbarho karshen hanyar gabashin yamma, a Arewacin karamar hukumar Ugheli dake jihart Delta.

Mutane shida ne suka kasance cikin motar yayinda hatsarin ta auku da misalin karfe 3:30 na yamma a ranar Sati.

Sannan uku daga cikin matafiyan, hade da direban sun tsere daga motar mai lamba Abuja DK 653 ABC, an rahoto cewa sauran mutane ukun sun mutu a hatsarin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel