Yan shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna duk da haramcin da gwamnati ta sanya kan haka (hotuna)

Yan shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna duk da haramcin da gwamnati ta sanya kan haka (hotuna)

Kungiyar Musulman Shi’a a ranar Talata, 18 ga watan Satumba sun yi zanga-zanga kan cigaba da tsare shugaban su, Ibrahim El-zakzaky.

Legit.ng ta tattaro cewa mambobin kungiyar sun cigaba da zanga-zangarsu a Kaduna duk da haramcin da gwamnati ta sanya kan ayyukansu da sauran zanga-zanda a jihar.

Masu zanga-zangan sun fara zanga-zanga da misalin karfe 1:15 na rana sannan sunyi tattaki daga hanyar Poly zuwa Kasuwan Bacci dauke da kwalayen sanarwa, inda suke wakar “gwamnati ta saki Zakzaky” da ‘Allahu Akbar”.

Yan shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna duk da haramcin da gwamnati ta sanya kan haka (hotuna)
Yan shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna duk da haramcin da gwamnati ta sanya kan haka
Asali: Original

Yan shi’an sun kammala zanga-zangar ne bayan sun kai shataletalen Kasuwan Bacci.

Yan shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna duk da haramcin da gwamnati ta sanya kan haka (hotuna)
Yan shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna duk da haramcin da gwamnati ta sanya kan haka
Asali: Depositphotos

Sai dai an lura da abu biyu, masu zanga-zangar basu yi amfani da bakaken kayan da aka sansu da shi ba sannan babu mata da yara a cikinsu.

Yan shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna duk da haramcin da gwamnati ta sanya kan haka (hotuna)
Yan shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna duk da haramcin da gwamnati ta sanya kan haka
Asali: Original

KU KARANTA KUMA: APC ta shirya makarkashiya don tsige Saraki da Dogara – CUPP

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 18 ga watan Satumba ya sha alwashin yin duk abunda zai iya domin tabbatar da dawowar Leah Sharibu daya daga cikin yan matan makarantar Dapchi 100 da yan ta’addan Boko Haram suka sace a jihar Yobe a farkon shekarar nan cikin koshin lafiya.

Yayinda dukkanin sauran yan makarantar suka tsira daga hannun yan ta’addan, yan Boko Haram sun cigaba da tsare ta bayan taki barin addinin ta na Kirista.

Legit.ng ta tattaro cewa shugaban kasar ya bayar da tabbacin ne a wasu rubutu day a wallafa a shafin twitter.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel