Kungiyar yan Najeriya dake zaune a kasar Amurka sun bukaci a bari su biya kudinfansar Leah Sharibu
- Kungiyar yan Najerya mazauna Amurka sun bukci gwamnati ta bari su iya kudin fansar Leah Sharibu
- Yan ta'addan Boko Haram sun yi barazanar kashe Leah nan da wata guda
- Leah Sharibu ta kasance yar makarantar Dapchi da ta rage a hannun yan ta'addan
Wata kungiyar yan Najeriya mazauna Amurka ta yi zanga-zanga akan barazanar kashe Leah Sharibu da yan ta’addan Boo Haram suka yi inda suka bukaci gwamnatin tarayya da ta bari kungiyoyin dake da ra’ayin biyan kudin fansa domin a sake a suyi.
Kungiyar tayi zargin cewa ta nemi majalisar dinkin dunya ta san baki, lokacin da a samu labarin shirin kashe ta da yan Boko Haram ke yunkurin yi amma suyi korafin cewa babu abunda akayi akai.

Asali: Depositphotos
Sunce hankalinsu ya tashi matuka da suka samu labarin kashe daya daga cikin ma’aikatan bayar da agaji, Saifura Ahmed da yan ta’addan suka yi.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar yan ta’addan Boko Haram sun yi barazanar kashe Leah Sharibu, yan makarantar Dapci dake jihar Yobe guda daya tilo da ta saura a hannunsu cikin 119 da aka sace a watan Fabrairu.
Barazanar na zuwa ne yayinda gamayyar kungiyar Boko Haram suka kashe Saifura Ahmed, daya daga cikin ma’aikatan agaji uku da aka sace a Rann, karamar hukumar Kala Balge.
KU KARANTA KUMA: Yan shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna duk da haramcin da gwamnati ta sanya kan haka (hotuna)
A cewar shafin The Cable, an sace Ahmed ne a lokaci wata mamaya da aka kai sansanin soji a yankin a ranar 1 ga watan Maris.
Akalla sojoji hudu, jami’an yan sanda da ma’aikatan hukumar agaji uku aka kashe a harin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng