Bari na sake baku tabbacin cewa babu wadda za’a bari a baya – Shugaba Buhari

Bari na sake baku tabbacin cewa babu wadda za’a bari a baya – Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya sha alwashin yin duk abunda zai iya domin tabbatar da dawowar Leah Sharibu daga hannun Boko Haram

- Yan Boko Haram sun cigaba da tsare ta bayan taki barin addinin ta na Kirista

- Buhari ya bayar da tabbacin ne a wasu rubutu da ya wallafa a shafin twitter

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 18 ga watan Satumba ya sha alwashin yin duk abunda zai iya domin tabbatar da dawowar Leah Sharibu daya daga cikin yan matan makarantar Dapchi 100 da yan ta’addan Boko Haram suka sace a jihar Yobe a farkon shekarar nan cikin koshin lafiya.

Yayinda dukkanin sauran yan makarantar suka tsira daga hannun yan ta’addan, yan Boko Haram sun cigaba da tsare ta bayan taki barin addinin ta na Kirista.

Bari na sake baku tabbacin cewa babu wadda za’a bari a baya – Shugaba Buhari
Bari na sake baku tabbacin cewa babu wadda za’a bari a baya – Shugaba Buhari
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa shugaban kasar ya bayar da tabbacin ne a wasu rubutu da ya wallafa a shafin twitter.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da kisan Saifura Hussaini Khorsa, wata ma’aikaciyar akaji da yan ta’addan Boko Haram suka yi inda ya bayyana hakan a matsayin rashin imani.

KU KARANTA KUMA: Tsayar da Buhari da mayakan Niger Delta suka yi ya tabbatar da karbuwarsa a fadin kasar - BCO

Yan ta’addan Boko Haram sun sace Khorsa, wacce ke aiki da hukumar bayar da agajin gaggawa watanni shida da suka gabata a sansanin yan gudun hijira na Rann dake jihar Borno.

Shugaban kasar yayi tofin Allah wadai din ne a wata sanarwa da babban hadiminsa, Malam Garba Shehu ya saki a Abuja a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel