Ku haramta shigar banza a Najeriya – Fasto ga gwamnati

Ku haramta shigar banza a Najeriya – Fasto ga gwamnati

- Fasto Amos Olugbenga yayi kira ga gwamnati da ta haramta shigar banza a Najeriya

- Ya nuna danasani kan cewa shigar banza ya fara mayar da kasar zuwa inda mutun zai iya aikata abunda ya ga dama

- Malamin yayi kira ga gwamnati, iyayi, shugabannin addinai da yan jarida da su yi kamfen kan adawa da shigar banza domin magance wannan mumunan dabi’a

Fasto Amos Olugbenga na cocin Christ Kingdom, Ilorin yayi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su sanya dokar da zai yi duba ga shigar banga a kasar.

Olugbenga yayi kiran ne a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Ilorin a ranar Talata, 18 ga watan Satumba.

Ku haramta shigar banza a Najeriya – Fasto ga gwamnati
Ku haramta shigar banza a Najeriya – Fasto ga gwamnati
Asali: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa ya lura cewa shigar banza ya zamo rowan dare a tsakanin matasa a kasar, cewa hakan na dakushe al’adu da martaban kasar daga zukatan yaran zamani.

Malamin ya nuna danasani kan cewa shigar banza ya fara mayar da kasar zuwa inda mutun zai iya aikata abunda ya ga dama, ta yadda mutun zai yi shigar da ya ga dama ba tare da la’akari da martabar kasar ba.

KU KARANTA KUMA: EFCC da Jami’an Kwastam sun yi wa Fayose kofar-raggo

Don haka malamin yayi kira ga gwamnati, iyayi, shugabannin addinai da yan jarida da su yi kamfen kan adawa da shigar banza domin magance wannan mumunan dabi’a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel