Kada Buhari ya kuskura yayi takara a zaben 2019 – Babban limamin coci

Kada Buhari ya kuskura yayi takara a zaben 2019 – Babban limamin coci

- Wani limamin coci yayi gargadi akan kudirin sake takara na Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Bishop Stephen Oni yace tsoffin yan siyasa su tarkata yanasu-yanasu su barwa matasa fage

- Yace wasu yan siyasan Najeriya sun dade akan mulki cewa hakan na daya daga cikin matsalolin kasar

Wani babban limamin cocin Anglican, Stephen Oni, yace kasar nan na bukatar matashi kuma mutun mai hangen nesa da zai zamo shugaban kasar na gaba sannan kuma ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya ajiye kudirinsa na sake takara a zaben 2019.

Yayi korafin cewa wasu yan siyasan Najeriya sun dade akan mulki sannan sun ki sauka daga matsayinsu domin ba matasa dama, inda ya bayyana hakan a matsayin daya daga cikin matsalolin da kasar ke fuskanta.

Kada Buhari ya kuskura yayi takara a zaben 2019 – Babban limamin coci
Kada Buhari ya kuskura yayi takara a zaben 2019 – Babban limamin coci
Asali: Depositphotos

Bishop Oni ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da sabon shugaba da sauran jami’an cocin Cathedral Church of St Stephen, Oke-Aluko, jihar Ondo.

Yayi korafi akan ci gaba da kasancewar tsofaffin yan siyasa akan dukkanin matakai na gwamnati inda yace wasu yan siyasar ma daura kansu suke akan mulki ta karfin tuwo.

KU KARANTA KUMA: Kana da karfin zuciya – PDP ga Dogara yayinda ya dawo jam’iyyar

Akan kudirin shugaba Buhari na sake takara a zabe mai zuwa, yace “yana da yancin sake takara, amma shawarata gare shi, idan zai yi da kyau, ya koma gida cikin farin ciki."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel