EFCC na mayyar farautan yan jam’iyyar adawa ne - Wike

EFCC na mayyar farautan yan jam’iyyar adawa ne - Wike

- Gwamnan jihar Rivers ya zargi hukumar EFCC da mayyar farautar yan siyasa masu adawa

- Wike yace babu inda aka taba ji hukumar yaki da rashawar ta ambaci wani dan APC da sunan bincike

- Yace ba zai taba bari hukumar ta janye masa hankali daga aikin da yake yi ba

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya zargi hukumar EFCC da mayyar farautar yan siyasa dake jam’iyyar adawa ne kawai.

Wike ya yi wannan zargin ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba yayin da yake hira da da tashar Channels TV.

EFCC na mayyar farautan yan jam’iyyar adawa ne - Wike
EFCC na mayyar farautan yan jam’iyyar adawa ne - Wike
Asali: Depositphotos

Gwamnan, har ila yau, ya karfafa cewa hukumar baza ta janye mishi hankali ba daga shirinsa na binciken jihohi dake da alaka da rashawa.

Yace, ‘’hukumar EFCC bata isa ta dauke mun hankali ba. Kudade da hukumar take bincike suna da alaka da jam’iyyar adawa.

‘’Kun taba ganin inda EFCC ta yi magana, game da da jam’iyyar APC mai mulki, ko an taba ji sunce mun gano cewar kudaden wannan zaben ya fito ne ta hannun gwamnati?"

KU KARANA KUMA: Dalilin da yasa na dakile tazarce na a matsayin gwamna - Tambuwal

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana karara tare da bayar da tabbacin cewa ba zai nemi takarar kujerar mataimakin shugaban kasar nan ta Najeriya ba a zaben 2019 sabanin yadda ake faman yadawa a lunguna da sako na kasar nan.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, jiharsa ta Ribas ita ya sanya a gaba duk da cewar wasu daga cikin manema takarar shugaban kasar nan su yi ma sa tayi tare da romon baka na kwadaitar da shi kan kasancewa abokin takararsu a yayin da suke shawagi da neman goyon bayansa.

Yayin ganawarsa da manema labarai a fadar gwamnatinsa dake birnin Fatakwal a ranar Alhamis din da ta gabata, Gwamna Wike ya bayyana cewa akwai manema takarar kujerar shugaban kasa da suka dauki alkawarin zai zamto mataimakin su amma ya hau kujerar na ki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel