Kotu ta tsare miji a kurkuku bisa zargin kashe matar sa a Minna

Kotu ta tsare miji a kurkuku bisa zargin kashe matar sa a Minna

Wata kotun Majistare dake garin Minna, babban birnin Jihar Niger, ta bada umarnin a garkame wani magidanci a kurkuku, sakamakon zargin sa da ake yi da hannun a mutuwar matar sa.

Sai dai kuma wanda ake zargin mai suna Ilesanmi ya musanta zargin da ake masa na hannu a kisan matar tasa.

Mai gabatar da kara, Aliyu Malami, ya shaida wa kotu cewa wata mata ce mai suna Blessing Kunle ta kai karar Ilesanmi a Ofishin ‘Yan sanda na Suleja.

Malami ya ce wanda ake tuhumar ya gaura wa matar sa mai suna Patience kutufo, daga wani dan sabani da ya shiga a tsakanin su, a ranar 31 ga watan Agusta, da misalin karfe 9:30 na dare.

Kotu ta tsare miji a kurkuku bisa zargin kashe matar sa a Minna
Kotu ta tsare miji a kurkuku bisa zargin kashe matar sa a Minna
Asali: Facebook

Ya ce naushin da ya yi wa matar ta sa ya sa jini ya rika fitowa ta kunnuwar ta da kuma bakin ta, har aka garzaya da ita asibitin Suleja, inda ta mutu a can.

Mai Shari’a Ibrahim ya ki amincewa da ja-in-jar da Ilesanmi ya yi cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar ballantana a hukunta shi.

KU KARANTA KUMA: Kada ku zabi wadanda zasu mayar da ofishin gwamna wajen rawar nanaye – Oshiomhole ya gargadi mutanen Osun

Daga nan sai ya bada umarni ‘yan sanda su yi kwafen karar guda su aika wa Daraktan Gabatar da Kararraki na Jiha, domin a nemi shawarar sa.

Ya ce a ci gaba da tsare wanda ake zargin har zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, sannan a cigaba da sauraron karar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng