Ganduje ya mayar da fam dinsa na takara, yace yana tare da zaben fidda gwani na kato-bayan-kato

Ganduje ya mayar da fam dinsa na takara, yace yana tare da zaben fidda gwani na kato-bayan-kato

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya mayar da fam dinsa na ra’ayin takarar kujerar gwamna a zaben 2019 sakatariyar All Progressives Congress (APC) dake Abuja.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole ne ya karfi fam din daga hannun gwamnan.

Ya samu rakiyan Sanata Barau Jibrin, tsohon ministan ilimi, Malam Ibrahim Shekarau, yan majalisar dokoki masu ci da sauran yan takaran da suka mayar da fam dinsu.

Ganduje ya mayar da fam dinsa na takara, yace yana tare da zaben fidda gwani na kato-bayan-kato
Ganduje ya mayar da fam dinsa na takara, yace yana tare da zaben fidda gwani na kato-bayan-kato
Asali: Depositphotos

Ganduje wanda ya ba shugaban jam’iyyar na kasa tabbacin cewa mutanen Kano na tare da shi da Shugaba Buhari, yace sun dauki tsarin zaben fidda gwani na kato-bayan-kato domin ba duk mambobin jam’iyyar damar zabar shugabanninsu.

A halin da ake ciki, wani jigon jam’iyyar APC a jihar Jigawa, Alhaji Hashim Ubale Yusuf ya bayyana cewa zai yi takarar kujeran gwamna domin ya gyara barnar da gwamnan jihar mai ci, Muhammad Abubakar Badaru ya haddasa.

KU KARANTA KUMA: Na hada kai da wani malamin tsubbu don muyi kudi da mai koyon aiki a wurina – Mai magani

Da yake zantawa da manema labarai a jiya Alhamis, 3 ga watan Satumba a jihaar Kano, Yussuf yayi zargin cewa gwamnan jihar Jigawa ya dauki wata hanya ta daban daga wacce kundin tsarin mulkin APC ke kai.

Yayi ikiarin cewa gwamnatin Badaru a Jigawa ta gaza a yankunan noma, lafiya, ilimi da kuma tsaro.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel