NADCEL: An Gano Sabuwar Hanyar da Ake Damfarar Ƴan Najeriya da Sunan Rundunar Soji

NADCEL: An Gano Sabuwar Hanyar da Ake Damfarar Ƴan Najeriya da Sunan Rundunar Soji

  • Rundunar sojojin Najeriya ta gargadi jama’a kan wasu bata gari da aka gano suna damfarar mutane kudi da suna bikin NADCEL 2026
  • Sojojin sun ce masu laifin na amfani da takardu na bogi da sunan rundunar wajen tura bukatun tallafi ga mutane da kungiyoyi
  • Rundunar sojin ta bayyana cewa duk wani mutum ko kungiya da ke neman kudi daga jama'a ba da sahalewar jama'a ba damfara ce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta gargadi jama’a kan wasu mutane da kungiyoyin masu laifi da take zargi da neman kudi ta hanyar yaudara da sunan bikin Ranar Sojin Najeriya (NADCEL) 2026.

Rundunar ta ce masu damfarar suna amfani da takardu na bogi da wasikun neman tallafi wajen yaudarar mutane, cibiyoyin hada-hadar kudi, kamfanoni da hukumomin gwamnati.

Sojoji sun gargadi mutane game da bullar wasu mutane da ke damfarar jama'a kudi da sunan bikin NADCEL 2026
Babban hafsan sojojin kasan Najeriya, Waidi Shaibu tare da dakarun OPSS. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Ana sojan gona da sojoji wajen damfara

Daraktar hulda da jama’a ta sojojin Najeriya, Kanar Appolonia Anele, ta fitar da sanarwa cewa, rundunar ta gano wasu mutane da ke karyar cewa su wakilan soji ne domin neman tallafin kudi, in ji rahoton Tribune.

Sanarwar ta ce masu laifin na aika wasiku da takardun neman daukar nauyin bikin NADCEL 2026 ba tare da izinin rundunar ba.

Runduna sojojin ta ce:

“Duk wani nau'in neman kudi, tallafi, gudummawa ko hadin gwiwa da ba hukumar sojin Najeriya ce ta amince da shi ba zamba ne.”

Bayani game da bikin NADCEL 2026

Rundunar ta bayyana cewa bikin NADCEL 2026 wani taron hukuma ne da aka shirya gudanarwa daga ranar 1 zuwa 6 ga Yuli, 2026 domin tunawa da cikar sojojojin Najeriya shekaru 163 da kafuwa.

Ta ce za a rika fitar da duk wata sanarwa ko bayani da ya shafi bikin ta kafafen sadarwa na rundunar da aka tabbatar.

Sojojin Najeriya sun bukaci jama’a, kamfanoni, cibiyoyin kudi da hukumomin gwamnati su rika tabbatar da sahihancin duk wani bukatar tallafi da ake yi da sunan rundunar kafin daukar wani mataki.

Rundunar ta gargadi jama’a da kada su amsa ko su biya wani kudin da ba a tabbatar da sahihancinsa ba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

“Sojojin Najeriya ba su amince ba, ba su goyi baya ba, kuma ba su ba da izinin tara kudi daga wasu mutane ko kungiyoyi da sunan rundunar ba.”

- Kanar Appolonia Anele.

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta dauki mataki mai tsauri kan wadanda ke damfara da sunanta.
Babban Hafsan sojojin kasan Najeriya, Waidi Shaibu tare da dakarun soji. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Masu laifi za su fuskanci hukunci

Rundunar ta kuma gargadi duk wanda aka samu yana sojan gona da sojojinta, kirkirar takardu na bogi ko tara kudi ta hanyar yaudara da sunan rundunar cewa zai fuskanci fushin doka.

Ta jaddada cewa za ta dauki matakan da suka dace domin kare martabar rundunar da kuma hana masu damfarar amfani da sunanta wajen cutar da jama’a.

An kama matashi dan damfara

A wani labari, mun ruwaito cewa, ‘yan sanda sun kama matashi a Kaduna da ake zargi da kwaikwayon muryoyin gwamnoni domin damfarar bayin Allah.

Kakakin rundunar, ASP Mansur Hassan ya tabbatar da kamen, inda ya ce Allah Ya yi wa matashin baiwar satar muryoyin jama'a, ciki har da ta manyan mutane.

ASP Mansur Hassan ya ƙara da cewa an samu matashin da lambobin wayar manyan mutane da ya damfara a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com