Cristiano Ronaldo Ya Kafa Sabon Tarihi a Gasar Cin Kofin Duniya Ta 2026

Cristiano Ronaldo Ya Kafa Sabon Tarihi a Gasar Cin Kofin Duniya Ta 2026

  • Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi a gasar Kofin Duniya bayan zama dan wasa na farko da ya zura kwallo har sau shida a gasar daban-daban
  • Dan wasan Portugal mai shekaru 41 ya zura kwallaye biyu a ragar Uzbekistan yayin da Portugal ta ci 5-0 a gasar
  • Ronaldo ya ci gaba da fafutukar lashe kofin Duniya, wanda shi ne babban kofi daya da ya rage a cikin manyan nasarorin rayuwarsa ta kwallon kafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Cristiano Ronaldo ya sake rubuta sunansa a tarihin kwallon kafa bayan ya zama dan wasa na farko da ya zura kwallo shida a gasar Kofin Duniya daban-daban.

Ronaldo ya kafa wannan tarihin ne a ranar Talata, yayin da Portugal ta yi wa Uzbekistan dakan sakwara da ci 5-0 a wasan rukuni na Kofin Duniya.

Kara karanta wannan

Kocin kungiyar kwallon kafa ya sha da kyar kan zargin satar mazakuta

Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tari a gasar cin kofin duniya ta 2026
Cristiano Ronaldo ya na murnar zura kwallo ta biyu a wasan Portugal da Uzbekistan a gasar Kofin Duniya 2026. Hoto: Maja Hitij - FIFA/FIFA via Getty Images
Source: Getty Images

Ronaldo ya zura kwallo a minti na 6

Wannan nasara ta taimaka wa Portugal wajen farfado da yakin neman lashe gasar, bayan da ta fara gasar da canjaras da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, in ji rahoton Sky Sport.

Dan wasan mai shekaru 41 ya fara zura kwallo a raga tun a minti na shida, bayan ya karbi kyakkyawan bugu daga João Cancelo inda ya tura kwallon ta wuce mai tsaron gidan Uzbekistan.

Wannan kwallo ita ce ta tara da Ronaldo ya ci a gasar Kofin Duniya tun lokacin da ya fara buga gasar a shekarar 2006 a Jamus.

Haka kuma, ita ce kwallo ta 144 da ya ci wa tawagar kasar Portugal a wasannin kasa da kasa.

Ronald ya karya wani tarihi na shekaru

Bayan wannan nasara, Ronaldo ya zama dan wasa na biyu mafi tsufa da ya taba zura kwallo a gasar Kofin Duniya, bayan Roger Milla na Kamaru wanda ya ci kwallo yana da shekaru 42 a gasar 1994.

Kara karanta wannan

Lionel Messi ya kere Ronaldo, ya kafa sabon tarihi a gasar cin kofin duniya

A minti na 39, Ronaldo ya sake zura kwallo ta biyu, inda ya kara tabbatar da mamayar Portugal kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Jaridar Punch ta rahoto cewa kafin hakan, Nuno Mendes ya kara wa Portugal kwallo ta biyu bayan wata kyakkyawar dabarar bugun tazara.

Rahoto ya nuna cewa Kofin Duniya shi ne babban burin Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo rike da kambun zakakurin dan wasa bayan tashi wasan Portugal da Uzbekistan a gasar Kofin Duniya 2026. Hoto: Alex Pantling - FIFA/FIFA via Getty Images
Source: Getty Images

Kofin Duniya ne babban burin Ronaldo

Duk da cewa Ronaldo ya lashe manyan kofuna da dama, ciki har da Gasar Cin Kofin Turai ta UEFA a 2016 tare da Portugal, har yanzu Kofin Duniya ne babban kofin da bai samu ba.

Tafiyar Ronaldo a gasar ta fara ne a 2006, inda ya taimaka wa Portugal kai wa wasan kusa da na karshe kafin ta kare a matsayi na hudu.

A gasar Kofin Duniya ta Qatar 2022, Ronaldo ya zama dan wasa na farko da ya zura kwallo a gasar sau biyar bayan ya ci wa Portugal bugun fenariti a karawarta da Ghana.

Messi ya kafa tarihi a gasar Kofin Duniya

A wani labari, mun ruwaito cewa, dan wasan Argentina, Lionel Messi, ya kafa sabon tarihi a gasar cin Kofin Duniya da ake gudanarwa a Amurka, Mexico da Canada.

Kara karanta wannan

Davido: Malamin Musulunci ya yi wa Rarara wankin babban bargo kan tsaro

Lionel Messi ya zuwa kwallo a wasan Argentina da Austria, wanda hakan ya sanya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a gasar cin Kofin Duniya.

Dan wasan gaba na Faransa, Kylian Mbappe zai iya karya wannan tarihi na Messi idan ya ci gaba da zura kwallaye a gasar musamman ganin bai kai sa shekaru ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com