Zan karbi sakamakon zaben fitar da gwani na PDP a duk yadda ya zo - Tambuwal

Zan karbi sakamakon zaben fitar da gwani na PDP a duk yadda ya zo - Tambuwal

- Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto yace zai karbi sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda za’a gudanar a watan Oktoba

- Tambuwal ya sha alwashin magance matsalar tsaro idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa

- Tsohon kakakin majalisar wakilan na daga cikin yan takarar dake neman tikitin takara a karkashin PDP

Gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Aminu Tambuwal, yace zai karbi sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda za’a gudanar a ranakun 5 da 6 ga watan Oktoba a Port Harcourt.

Gwamnan ya bayyana hakan a ranar Talata, 18 ga watan Satumba a Birnin Kebbi lokacin da ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a kokarinsa na bayyana massa kudirinsa gabannin zaben fidda gwanin, kmfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito.

Zan karbi sakamakon zaben fitar da gwani na PDP a duk yadda ya zo - Tambuwal
Zan karbi sakamakon zaben fitar da gwani na PDP a duk yadda ya zo - Tambuwal
Asali: Depositphotos

Yayi alkawarin magance matsalolin tsaro a Zamfara, Birnin Gwari in Kaduna, Benue, Taraba da Kebbi idan suka marawa kudirinsa baya.

Mataimakin shugaban jam’iyyar, Alhaji Musa Argungu ya ba Tambuwal tabbacin cewa mambobin jam’iyyar zasu mara masa baya dari bisa dari.

KU KARANTA KUMA: Maye gurbin Adeosun da Zainab Ahmad: Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta caccaki Buhari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Gombe kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party’s (PDP), Ibrahim Dankwambo ya nuna jajircewarsa na son kawo karshen duk wani kashe-kashe na kabilanci da addini a fadin kasar, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 2019.

Dankwambo ya bayyana hakan a wata sanarwa da sanya hannun Dr Ayoade Adewopo, daraktan labarai na kungiyar kamfen dinsa a Abuja a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba.

Gwamnan yayi jaje ga wadanda harin kauyukan Gon, Nzumosu, Bolki, Nyanga da Bukuto dake karamar hukumar Numan na jihar Adamawa ya cika dasu, inda aka kashe malami da wasu mutane 51.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel