Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyeama, ya soki lamarin kasar Switzerland cewa ta na da hannu a badakalar boye makudan kudade da tsohon shugaba na mulkin soja, Sani Abacha ya yi a kasar a lokacin ya ke kan mulki.
Danladi Matawal darakta janar na cibiyar binciken gine-gine da titina, ya yi gargadi kan cewa kada gwamnatin Najeriya ta yi wa lamarin da ya faru na girizan kasa a babban birnin tarayya, Abuja rikon-sakainar-kashi.
Jami’an hukumar kwastam na Najeriya, a jihar Imo ta kama babban mota shake da buhuhunan shinkafa 200 da aka boye da sinkin ayaba. Shugaban kwastam na yankin Zone C, Kayode Olusemire, yace an kama motar kwantanan a karshen mako.
Mazauna Lafia babban birnin jihar Nasarawa sun shiga tashin hankali a yau Litinin, 10 ga watan Satumba wani gidan mai kama da wuta sakamakon fashewar iskar gas. NAIJ.com ta tattaro cewa wadanda ke tashan man duk sun kone.
Wata kungiyar matasan jihar Kwara, a ranar Asabar, 8 ga watan Satumba yayinda take karfafa gwiwar sauran yan siyasan Najeriya da suyi koyi da tsarin shugabanci irin na shugaban majalisar dattawa sun shirya matasa don yin gangami
Yan takaran kujerar gwamna guda bakwai karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun yanki fam din takara a jihar Nasarwa, sannan kuma yan takarar wannan kujera biyar ne suka yanki fam a jam'iyyar PDP.
Dr. Grace Olasumbo, wata shahararriya a fannin lafiyar abinci ta shaawarci yan Najeriya das u hankalita da kayan marmari da gayayyaki masu kaloli daban-daban musamman idan yazo a kalolin shudi da dorawa a hade.
Dan takaran shugaban kasa a PDP Taminu Turaki, a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba, ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar zata bi ta kan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan kudirin gyara dokar zabe da yayi watsi dashi.
Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Walid Jibrin ya bayyana cewa kwamitin na duba ga yiwuwar rage yawan yan takaranta na shugaban kasa, saboda gujema yiwuwar barkewar rikici.
Aisha Musa
Samu kari