EFCC za Ta Gurfanar da Shugaban Fulani na Miyetti Allah bayan Cafke Shi
- Hukumar EFCC na zargin shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, Bello Bodejo da laifin da ya shafi kuɗi da suka kai dala miliyan 2.53
- EFCC na zargin cewa Bello Bodejo ya karɓi wasu manyan kuɗi a hannun tsohon Akanta Janar na jihar Bauchi ba tare da cika ka'ida ba
- Rahotanni sun nuna cewa tuhume-tuhume guda 12 ne EFCC ta shigar a kan shugaban kungiyar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar EFCC na shirin gurfanar da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hóre, Bello Bodejo, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Rahoto ya nuna cewa za a gurfanar da shi ne bisa zargin hannu a harkokin tallafa wa ta'addanci da kuma almundahanar kuɗi da suka kai kimanin dala miliyan 2.53.

Source: Facebook
Zargin da ake yi wa Bodejo
A sakon da ta fitar a Facebook, hukumar EFCC ta shigar da tuhume-tuhume guda 12 a kansa a ranar 22 ga Yuni, 2026.
EFCC ta zarge shi da karɓa da kuma mallakar manyan kuɗin ƙasashen waje da ake zargin sun samo asali ne daga ayyukan da suka saɓa wa doka, wanda ya ci karo da tanade-tanaden dokokin hana almundahana na 2011 da 2022.
A wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Laraba, ya ce ana sa ran Bodejo zai gurfana a kotu domin amsa laifuffukan da ake tuhumarsa da su da zarar an sanya ranar fara shari'a.
EFCC ta ce Bodejo ya karɓi kuɗi masu yawa a wajen tsohon Akanta Janar na Jihar Bauchi, Sa’idu Abubakar, ba tare da bi ta hanyar cibiyar kuɗi kamar yadda doka ta tanada ba.
Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya ce a ranar 11 ga Janairu, 2022, Bodejo ya karɓi dala 100,000 a tsabar kuɗi daga Sa’idu Abubakar a Abuja, adadin da ya zarce iyakar kuɗin da doka ta amince a yi mu'amala da su a hannu.
Karin tuhumar da ake masa
Punch ta wallafa cewa wata tuhumar kuma ta ce ya karɓi dala 200,000 a tsabar kuɗi daga mutumin a ranar 21 ga Janairu, 2022.
Har ila yau, EFCC ta zarge shi da karɓar dala 500,000 a ranar 20 ga Maris, 2024, da kuma dala 980,000 a ranar 7 ga Fabrairu, 2024, duk a hannu ba tare da bi ta banki ba.

Source: Twitter
A tuhuma ta 10, hukumar ta ce Bodejo ya mallaki dala 980,000 a Abuja a ranar 7 ga Fabrairu, 2024, a yanayin da ya kamata ya san ko ya fahimci cewa kuɗin na iya kasancewa ribar ayyukan da suka saɓa wa doka.
An daga shari'ar El-Rufa'i
A wani labarin, kun ji cewa an dage shari'ar da ake yi tare da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i zuwa Satumban 2026.
An bayyana cewa Nasir El-Rufa'i zai cigaba da zama a hannun hukuma har zuwa lokacin da za a dawo kotu domin cigaba da shari'ar.
Hakan ya biyo bayan gaza cika sharudan beli da El-Rufa'i ya yi ne, inda jama'a ciki har da Sarki Sanusi II suka ce sun yi matukar tsauri.
Asali: Legit.ng

