Yanzu Yanzu: El-Rufai, Okorocha da sauran gwamnonin APC su isa Abuja domin a tantance su (hotuna)
- Wasu gwamnonin APC sun gabatar da ansu domin a tantance su
- Daga cikin wadanda suka bayyana akwai Nasir Ahmad El-Rufai da wasu gwamnoni
- Tantancewar zai gudana ne a yau Alhamis, 20 ga watan Satumba a Abuja
An gano Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna tare da sauran gwamnonin jiha karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba zaune a inda suke jiran kwamitin tantancewa na jam’iyyar ta tantance su gabannin zaben fidda gwani na 2019.
Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo da Abdullahi Ganduje na Kano na daga cikin mutanen da suka hallara domin tantancewar.

Asali: UGC

Asali: Depositphotos

Asali: Depositphotos
KU KARANTA KUMA: Sabon rikici ya kunno kai a PDP kan zargin wani dan takarar shugaban kasa na yi ma APC aiki
Da farko Legit.ng ta rahoto cewa APC ta sanar da cewar zata fara tantance yan takarar ta na dukkan matakai na jihad a tarayya a ranar Laraba, 19 ga watan Satumba.
Za’a kammala shirin ne a ranar Juma’a 21 ga watan Satumba. Ana sanya ran gwamnoni da yan takara na tarayya su kasance a Abuja domin tantancewar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng