An Samu Sauki: Matatar Dangote Ta Rage Farashin Fetur da N50 kan Kowace Lita

An Samu Sauki: Matatar Dangote Ta Rage Farashin Fetur da N50 kan Kowace Lita

  • Matatar Dangote ta rage farashin litar fetur da take sayar wa 'yan kasuwa da N50, inda ta sauke farashin daga N1,175 zuwa N1,125
  • Kamfanin ya ce faduwar farashin mai a duniya sakamakon lafawar rikicin Gabas ta Tsakiya ne ya jawo ta sauke farashin man ta
  • Ana sa ran 'yan kasuwar mai na cikin Najeriya za su sauke farashin litar fetur din a gidajen mansu domin saukaka wa al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas - Matatar man Dangote ta sanar da rage farashin fetur da N50 a kan kowace lita, a wani mataki da ake sa ran zai shafi farashin da ‘yan kasuwa ke sayar da mai a Najeriya.

A sanarwar da kamfanin ya fitar ga abokan huldarsa, matatar ta ce ta rage farashin da take sayar wa ‘yan kasuwa daga N1,175 zuwa N1,125 a kowace lita.

Kara karanta wannan

"Ba mu ji dadi ba"; Wike ya aika sako ga Super Eagles kan gaza zuwa gasar cin kofin duniya

Matatar Dangote ta sauke farashin fetur.
Wata mata na sayar da fetur a gidan mai, tana cike da farin ciki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dangote ya rage farashin man fetur

Baya ga rage farashin da ake ba 'yan kasuwa a rumbunan ajiyar mansa, Dangote ta kuma rage farashin samar da fetur ta hanyar tashar ruwa, in ji rahoton The Cable.

Kamfanin ya ce a halin yanzu, ya sauya farashin daga N1,495,215 a kan kowane tan zuwa N1,428,165 don daidaita farashin da kasuwar waje.

Matatar ta ce wannan matakin ya biyo bayan saukin rikice-rikicen da ake samu a Gabas ta Tsakiya, wanda ya taimaka wajen rage farashin makamashi a kasuwar duniya.

Abin da Dangote ya ce kan farashin mai

Matatar Dangote ta bayyana cewa tana ci gaba da kokarin samar da fetur cikin sauki tare da inganta ayyukanta a kasuwar man fetur da aka bude a Najeriya.

Kamfanin ya ce:

“Muna ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da samun kayayyaki cikin aminci yayin da muke taka rawa wajen sauya yanayin farashi a kasuwar man fetur ta Najeriya.”

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto mutane sama da 40 da 'yan ta'addan ISWAP suka sace a Borno

Wannan shi ne karo na biyu da matatar ta rage farashin fetur cikin kasa da mako guda.

A baya, matatar ta rage farashin kowace lita da N75, inda ta saukar da shi daga N1,250 zuwa N1,175, yayin da ta danganta matakin da lafawar rikicin Gabas ta Tsakiya.

A farkon shekarar nan, matatar ta taba kara farashin fetur sakamakon karuwar farashin danyen mai a duniya da matsalolin samar da mai da suka biyo bayan rikicin yankin.

Ana sa ran masu gidajen mai za su rage nasu farashin bayan matakin Dangote.
Mutane sun yi dandazo a gidan mai domin sayen fetur. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tasirin faduwar farashin mai a duniya

Raguwar farashin danyen mai a kasuwar duniya ya taimaka wajen rage kudin samar da fetur ga matatun mai, kamar yadda rahoton Business Day ya nuna.

Rahotanni sun nuna cewa farashin gangar danyen mai na Brent ya sauka zuwa dala $72.97, wanda shi ne mafi karanci tun watan Fabrairu lokacin da rikicin ya fara.

Ana sa ran sabon farashin na Dangote zai yi tasiri kan farashin da manyan dillalan mai da gidajen mai ke amfani da shi a fadin Najeriya yayin da suke sabunta farashin sayar da fetur.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki manoma a Kaduna, an kashe bayin Allah

Hasashen CBN kan farashin mai a 2026

Tun da fari, mun ruwaito cewa, CBN ya yi hasashen yadda farashin man fetur zai kasance a shekarar 2026, duk da sauye-sauyen da ake samu a kasuwar mai a cikin gida.

Hasashen ya dogara ne kan yanayin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, musayar kuɗin kasashen waje da kuma yawan man da ake samarwa a Najeriya a kullum.

Saukar farashin man fetur da matatar Dangote ta janyo a baya na iya fuskantar barazana, idan aka samu koma baya a samar da mai ko kuma aka koma dogaro da shigo da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com