Za a hukunta masu yi wa mata saki uku a lokaci guda a kasar Indiya

Za a hukunta masu yi wa mata saki uku a lokaci guda a kasar Indiya

Majalisar zartarwa ta kasar Indiya ta yi na’am da tsatsaurar dokar nan da ta haramta yi wa mata saki uku a lokaci daya.

Ministan doka na kasar Ravi Shankar Prasad ya bayyana cewa daga yanzu za a dunga zartar da hukunci ga duk mutumin da ya yi wa matarsa saki uku lokaci daya.

Yin saki uku lokaci guda ya zama tamkar ruwan dare a tsakanin mazajen Musulmi.

Za a hukunta masu yi wa mata saki uku a lokaci guda a kasar Indiya
Za a hukunta masu yi wa mata saki uku a lokaci guda a kasar Indiya
Asali: Getty Images

A cewar ministan, majalisar zartarwar ta yarda da dokar ne sakamakon yadda maza ke cigaba da gudanar da irin wannan saki duk kuwa da hukuncin da majalisar kolin kasar ta zartar na haramta yin hakan.

Gwamnatin Indiya ta dade tana kokarin ganin majalisar dokokin kasar ta yarda da hukuncin daurin shekara uku ga duk mutumin da ya keta wannan doka.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnan jihar Kano ya rantsar da sabon mataimakin gwamna

Sai dai 'yan hamayya na so a yi a dokar gyaran fuska ta yadda ba za a yi amfani da ita wajen matsawa jama'a ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel