Ziyarar Theresa May ba ya yana nufin tsayar da Buhari bane – Hukumar Birtania

Ziyarar Theresa May ba ya yana nufin tsayar da Buhari bane – Hukumar Birtania

Babban hukumar kasar Birtaniya a Najeriya tace ziyarar da Theresa May, Fiaye Ministar Birtaniya ta kawo kwanan nan, ba yana nufin tsayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari kowani dan takara bane.

Laura Beaufils, mataimakiyar kwamishinan Birtaniya a Najeriya, ta bayyana hakan a jawabin da tayi a wani taron tattauanwa da hukumar ta shiryawa yan jarida a Lagas a ranar Juma’a.

Ta kuma bayyana jajircewar gwamanatin Birtaniya wajen kashe Euro miliyan 47.4 a shirin zurfafa damokradiyya a Najeriya.

Ziyarar Theresa May ba ya yana nufin tsayar da Buhari bane – Hukumar Birtania
Ziyarar Theresa May ba ya yana nufin tsayar da Buhari bane – Hukumar Birtania
Asali: UGC

Da take Magana a kan rawar ganin da Birtaniya ke takawa wajen zurfafa damokradiyyar Najeriya, Beaufils ta bayyana cewa gwamnatin Birtaniya bata da kudirin sanya hannu a sakamakon zaben 2019, ta kara da cewa babu wani dan takara da tafi so.

KU KARANTA KUMA: Zamu kashe Leah Sharibu nan da wata guda – Boko Haram sunyi barazana ga gwamnatin tarayya

Gwamnan jihar Gombe kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party’s (PDP), Ibrahim Dankwambo ya nuna jajircewarsa na son kawo karshen duk wani kashe-kashe na kabilanci da addini a fadin kasar, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 2019.

Dankwambo ya bayyana hakan a wata sanarwa da sanya hannun Dr Ayoade Adewopo, daraktan labarai na kungiyar kamfen dinsa a Abuja a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel