Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC sunyi gab da rasa matsayinsu na masu rinjaye a majalisar dokokin kasara a watan Yuli im kadan kafin majalisar dokokin ta fara hutun ta na shekara, sai dai tana ta kokarin kasancewa mafi rinjaye.
Wani dan takarar kujeran siyasa na APC a zaben fidda gwani da aka kammala a jihar Adamawa, Habila Istifanus ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, inda ya bayyana rashin adalci a zaben fidda gwani da aka kammala a matsayin hujjarsa.
Shugaban kungiyar magoya bayan shugaban kasa Buhari wato Buhari Presidential Support Committee (BPSC), Alhaji Ya’u Adamu dan Fulani, ya yi watsi da hasashen wasu malaman Najeriya game da sakamakon zaben 2019 me zuwa.
Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa fafutukar da ake yi a Najeriya tsakanin nagari da mugu, sannan kuma cewa ba tsakanin manyan addinan kasar biyu bane. Ya bayyana hakan a wani taro na kungiyar manyan malamai.
Yan Shi’a sun bayyana cewa ikirarin da ministan labarai, Lai Mohammed ya yi cewa gwamnatin tarayya na kashe naira miliyan 3.5 duk wata wajen ciyar da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shugaban kungiyar da ke tsare bai nuna a jikinsa ba.
Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa gwamnoni kadan ne za su iya biyan albashin N30,000 a matsayin mafi karancin albashi. Ya bayyana hakan ne a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, lokacin da ya ke jawabi..
Gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 7 ga watan Nuwamba ta bayyana cewa N30,000 na karancin albashi da ke kunshe rahoton kwamitin da Gwanatin ta kafa shawara ne har yanzu ba wai sun amince da shi bane, Ministan labarai ya bayyana.
Rundunar yan sandan Najeriya ta sallami jami’in ta da aka dauka a wani bidiyo bayan ya sha giya ya bugu. Bidiyon wanda ya yi fice sannan ya ke nuna jami’in dan sanda daga yankin Akowonjo, Dopemu da ke jihar Lagas ya ja hankali.
A yau Laraba, 7 ga watan Nuwamba ne aka sake gurfanar da shugaban kungiyar yan Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky karo na biyu a gaban babbar kotun jihar Kaduna domin ci gaba da shari’ar da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar akan shi
Aisha Musa
Samu kari