Yadda Isra’ila Ta Shirya Taimaka wa Zanga Zanga a Iran domin Kifar da Gwamnati

Yadda Isra’ila Ta Shirya Taimaka wa Zanga Zanga a Iran domin Kifar da Gwamnati

  • Tsohon Firaministan Isra’ila, Naftali Bennett, ya bayyana cewa kasar ta shigar da na’urorin Starlink a boye zuwa Iran
  • Bennett ya bayyana cewa an shirya samar da dubban na’urori domin tabbatar da ci gaba da intanet da kafafen sada zumunta a Iran
  • Ya zargi gwamnatin Benjamin Netanyahu da dakatar da shirin, lamarin da ya hana masu zanga-zanga cin gajiyar tsarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Tsohon Firaministan Isra’ila, Naftali Bennett, ya yi tone-tone game da yadda kasar ta shirya taimakawa masu zanga-zanga a Iran.

Benneth ya bayyana cewa Isra’ila ta shigar da na’urorin Starlink a boye zuwa cikin Iran yayin da ake zanga-zanga.

Yadda Isra'ila ta shirya taimaka wa masu zanga-zanga a Iran
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a Tel Aviv. Hoto: Taylor Hill.
Source: Getty Images

Ya yi wannan bayani ne yayin taron JNS International Policy Summit da aka gudanar a birnin Jerusalem, cewar Reuters.

Yadda Isra'ila ta yi safarar na'urori Iran

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Gwamnatin Tinubu ta kawo shaidu 30 da za su ba da shaida a kotu

Bennett ya ce shi ne ya fara wani shiri na saye da kuma safarar dubban na’urorin Starlink zuwa Iran.

A cewarsa, manufar shirin ita ce tabbatar da ci gaba da samun intanet da amfani da kafafen sada zumunta a kasar.

Iran ta taba zargin Isra’ila da Amurka da shigar da irin wadannan na’urori domin raunana tsaronta da zaman lafiyarta.

Ko da yake ba a ba Starlink lasisin aiki a Iran ba, mamallakin kamfanin, Elon Musk ya taba cewa ana amfani da wannan sabis din a kasar.

Bennett ya ce an tsara na’urorin ne domin bai wa masu zanga-zanga damar sadarwa da tsara ayyukansu cikin sauki.

Ya kara da cewa manufar ita ce taimaka musu wajen kalubalantar gwamnatin Iran da neman sauyi a kasar.

Sai dai ya zargi gwamnatin Firayim minista, Benjamin Netanyahu da kasa ci gaba da aiwatar da wannan tsari.

A cewarsa, lokacin da zanga-zangar ta barke, tsarin da aka shirya bai kasance a shirye ba saboda dakatar da aikin.

Ana zargin Netanyahu ya dakile wani shirin Isra'ila a Iran
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a birnin Tel Aviv. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Yadda aka katse intanet a Iran

Kara karanta wannan

'Ya kamata Isra'ila ta tsaya da kafarta': Netanyahu kan taimakon makamai daga Amurka

Ofishin Netanyahu bai fitar da martani kai tsaye kan kalaman Bennett ba a lokacin wallafa rahoton.

Hukumomin Iran sun sha katse intanet a lokutan rikice-rikice da zanga-zanga domin dakile yada bayanai tsakanin jama'a.

Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan Iran sun koma amfani da Starlink a lokutan da aka dakatar da intanet a kasar, cewar Al Jazeera.

Bennett, wanda ke cikin ‘yan adawa masu neman maye gurbin Netanyahu a zabe mai zuwa, ya bukaci karin hadin kai a yankin.

Ya ce kasashen Gabas ta Tsakiya su hada karfi wajen tunkarar gwamnatin Iran, wadda ya bayyana a matsayin mai rauni da rashin tasiri.

Bennett ya yi hasashen cewa gwamnatin Iran za ta fadi wata rana kamar yadda tsohuwar Tarayyar Soviet ta rushe a tarihi.

Netanyahu ya bayyana a gaban kotu

A baya, kun ji cewa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sake gurfana a kotun Tel Aviv bayan zarge-zargen da ake yi masa wanda ya dauki tsawon lokaci.

Netanyahu ya bayyana a gaban kotun karo har na 88 domin kare kansa daga tuhume-tuhumen rashawa da cin amanar ƙasa.

Alƙalan kotun sun dawo da zaman shari’ar ranar Talata saboda dalilan tsaro da jadawalin siyasar Netanyahu, yayin da aka mayar da hankali kan wani zargi daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.