Fafutukar da muke yi tsakanin nagari da mugu ne – Osinbajo
Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa fafutukar da ake yi a Najeriya tsakanin nagari da mugu, sannan kuma cewa ba tsakanin manyan addinan kasar biyu bane.
A cewar wata sanarwa daga babban mai bashi shawara a affin labarai , Mista Laolu Akande a ranar Lahadi, 11 ga watan Nuwamba, mataimakin shugaban kasar yayi jawabi a wani taro da kungiyar manyan malamai, reshen Ikeja, jihar Lagas suka shirya a ranar Asabar.
Ya shawarci shugabannin addinin da su ci gaba da fada ma mabiyansu cewa su rungumi zaman lafiya sannan su yi aiki don hadin kan kasar.
Osinbajo ya ce takatsantsan da gwamnatin nan ke yi wajen kashe kudi ya taimaka matuka wurin cimma nasara wajen yin ayyukan ci gaba fiye da na gwamnatocin baya.

Asali: Facebook
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta zuba jari sosai wajen kare al’umma, inda tace wannan ne mafi girma da ya taba faruwa a tarihin kasar.
KU KARANTA KUMA: Rigimar APC ta kara cabewa a Ondo bayan ‘Yan Majalisa sun yi watsi da zama da Gwamna
Mataimakin shugaban kasar ya kuma lissafa ayyukan ci gaba wanda suka hada da aikin jirgin kasa na Lagas-Kano, hanyar moota biyu na Lagas-Ibadan da kuma gadar Niger na biyu.
Ya kuma yi bayanin cewa ta shirin N-Power kadai matasa 500,000 ne suka amfana.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng