World Cup: Amurka Ta Sassauta Takunkumi kan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Iran

World Cup: Amurka Ta Sassauta Takunkumi kan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Iran

  • Yayin da ake ci gaba da gasar cin kofin duniya a Amurka, kasar ta sassauta takunkumi kan tawagar kwallon kafa ta Iran
  • Sabuwar dokar ta bai wa tawagar Iran damar shiga Amurka kwanaki biyu kafin wasansu na gaba maimakon kwana daya kadai
  • Iran ta nuna rashin jin dadi kan takunkumin, tana mai cewa hakan ya jefa tawagar cikin wahala yayin zirga-zirga tsakanin Mexico da Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Amurka ta sanar da sassauta wasu takunkumin tafiye-tafiye da aka sanya wa tawagar kwallon kafa ta Iran a gasar kofin duniya ta 2026.

Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta ce yanzu an bai wa tawagar damar shiga kasar kwanaki biyu kafin wasansu na gaba.

Iran ta samu sassauci a gasar cin kofin duniya
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Donald Trump na Amurka. Hoto: Anadolu Ajansi, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Yadda aka hana yan kwallon Iran shiga Amurka

Kara karanta wannan

Trump ya fadi sunayen masu safarar kudin ta'addanci a Najeriya, kasashe

Tun farko, an takaita wa ‘yan wasan Iran shiga Amurka ne kwana daya kacal kafin kowanne wasa da suke da shi, cewar Reuters.

Wannan mataki ya sa kocin tawagar Iran ya bayyana cewa su ne tawagar da aka fi tauye wa hakkoki a gasar.

A cewar kakakin Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida, za a ba Iran damar shiga Amurka kwanaki biyu kafin wasansu a Seattle.

Sai dai har yanzu za a bukaci tawagar ta fice daga Amurka a ranar da aka kammala wasan da suke yi.

Jami’an Amurka sun ce sauran matakan tsaro da ka’idojin da aka kafa ba su sauya ba duk da sassaucin.

Sun kara da cewa gwamnati na da burin tabbatar da tsaro ga ‘yan wasa, jami’ai da kuma magoya baya.

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, wato FIFA, da tawagar Iran ba su fitar da wata sanarwa kai tsaye ba.

Yan kwallon Iran sun samu sassauci daga Amurka
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Iran ta yi korafi kan takunkumin Amurka

A makon da ya gabata, Iran ta bayyana aniyarta ta kai karar wannan takunkumi ga FIFA saboda wahalhalun da suke fuskanta.

Kara karanta wannan

Trump ya kawo tsarin da kayan abincin Amurka zai rika zuwa Iran

Tawagar na yin zirga-zirga daga sansaninta da ke Tijuana a Mexico zuwa biranen Amurka kafin gudanar da wasanni, cewar CNN.

Takunkumin ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da tsamin dangantaka tsakanin Washington da Tehran bayan watanni na rikici.

A watan Maris, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Iran na da damar shiga gasar amma ba ya ganin dacewar ci gaba da zamanta tsakanin wasanni.

Ya bayyana cewa wannan matakin yana da alaka da tsaron tawagar da kuma kare lafiyar ‘yan wasan yayin gasar cin kofin duniya.

Sabon sassaucin da Amurka ta yi na nuna wani dan sauyi a yadda ake tafiyar da dokokin da suka shafi tawagar Iran a gasar.

Yan kwallon Iran sun samu damar shiga Amurka

A baya, an ji cewa Amurka ta bai wa tawagar ƙwallon ƙafar Iran bizar shiga Amurka gabanin gasar kofin duniya da za a fara mako mai zuwa, kamar yadda jami’an kasar suka fada.

An amince da bayar da bizar ne kwanaki 10 kacal kafin wasan farko na tawagar da New Zealand, wanda za a buga a Los Angeles ranar 15 ga Yunin 2026.

Amurka ta bayar da bizar da ake buƙata domin Iran ta shiga gasar kofin duniya, ciki har da ta ‘yan wasa da wasu ma’aikatan da za su tallafa masu a gasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.