Mafi karancin albashi: Kaso 95 bisa 100 na gwamnonin kasar nan ba za su iya biya ba – Gwamna Umahi

Mafi karancin albashi: Kaso 95 bisa 100 na gwamnonin kasar nan ba za su iya biya ba – Gwamna Umahi

Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa gwamnoni kadan ne za su iya biyan albashin N30,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Ya bayyana hakan ne a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin mutane 36 da za su duba yanayi da yiwuwar karin albashi a jihar.

Ya ce: “Kashi 95 bisa 100 na jihohin Najeriya ba su iya biyan N30,000 a matsayin mafi kankantar albashi ba, idan ma sun ce za su iya, toh duk yaudara ne.

“Idan ba a kara wa jihohi kudin da gwamnatin tarayya ke basu ba a duk wata ba, toh babu yadda za a yi su iya biyan karin albashi.

Mafi karancin albashi: Kaso 95 bisa 100 na gwamnonin kasar nan ba za su iya biya ba – Gwamna Umahi

Mafi karancin albashi: Kaso 95 bisa 100 na gwamnonin kasar nan ba za su iya biya ba – Gwamna Umahi
Source: Depositphotos

“A kowane wata gwamnatin tarayya na kwasar kashi 52 bisa 100 na kudaden shigar gwamnati. To a lokacin da na yi kokarin lissafa cewa bari na kididdiga idan na ce kananan hukumomi su biya naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi, sai na gano cewa a duk wata sai sun ramto naira bilyan 1 sun cika domin su biya albashi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mambobin majalisar wakilai sun koka kan rasa tikitin dawowa majalisa

“Ni dai ba zan taba zama gwamnan da ke daukar kudaden shiga daga gwamnatin tarayya kacokan gaba daya ina biyan albashi da su ba.

“Sai an sake duba batun biyan kudin tallafin man fetur sosai, a kasar nan, watau ‘subsidy’. Idan ana so a fahimci wani abu daga ribar danyen mai. Wannan gaskiya ce, amma sai wanda ya daure zai iya furta ta, domin idan mu na adana kudaden tallafin man fetur, to za a fahimci alherin abin.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel