Sanata Sani ya bayyana manyan kalubale ga zaben 2019, ya nemi a zuba a idanu da kyau
- Manyan yan Najeriya da dama na ta tofa albarkatun bakunansu akan zaben 2019 mai zuwa
- Sanata Shehu Sani ya bayyana ra’ayinsa akan zaben 2019 mai zuwa
- Sanatan mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya ya yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su zuba idanu sosai
Sanata Shehu Sani ya bayyana ra’ayinsa akan zaben 2019 mai zuwa, inda ya bayyana manyan kalubale biyu ga zaben.
Sanatan mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya ya yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su zuba idanu sosai gabannin zaben.

Asali: Depositphotos
A cewarsa yawan yadda ake amfani da kudin al’umma wajen siyan kuri’u da masu jefa kuri’u da kuma yadda ake amfani da jami’an tsaro wajen razana yan adawa, sune manyan kalubale ga zaben mai zuwa.
A wani lamari na daban, mun ji cewa Majalisar dattawan Najeriya ta daga zama a yau Talata, 13 ga watan Nuwamba, 2018 na tsawon mako daya sakamakon rashin halartar sanatoci zaman majalisar da aka saba.
KU KARANTA KUMA: Dogara dan siyasa ne mara karfi a Bauchi – Gwamna Abubakar
Zauren majalisar na bukatar akalla sanatoci 38 kafin a iya zantar da wani abu, amma jaridar Punch ta bada rahoton cewa sanatoci 20 kacal cikin 109 ne suka halarci zauren a yau.
Bulaliyar maras rinjaye a majalisar, Sanata Philip Aduda, wanda ya bada shawaran daga zamar ya yi bayanin cewa yawancin sanatocin sun tafi ayyukan duba ma'aikatun gwamnati.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng