Yadda Tsohon Minista a Gwamnatin Tinubu Ya Yi Watsi da Gayyatar Hukumar ICPC

Yadda Tsohon Minista a Gwamnatin Tinubu Ya Yi Watsi da Gayyatar Hukumar ICPC

  • Tsohon ministan kirkire-kirkire da fasaha, Uche Nnaji, ya yi watsi da gayyata da dama daga hukumar ICPC
  • Takardun da aka gano sun nuna ICPC ta aika masa gayyata ta WhatsApp, imel da saƙonnin tunatarwa
  • Bayan ya ƙi amsa gayyata sau da dama, kotun tarayya da ke Abuja ta umarci a kama shi domin ci gaba da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rahotanni sun nuna cewa tsohon Ministan Kirkire-kirkire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya yi watsi da gayyata da dama daga Hukumar ICPC.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa hukumar ta tura masa gayyatar saboda zargin mallakar takardun bogi na digirin fako da kuma bautar kasa wato NYSC.

Kara karanta wannan

Kocin kungiyar kwallon kafa ya sha da kyar kan zargin satar mazakuta

ICPC ta tura gayyata ga tsohon minista zargin mallakar takardun bogi
Shugaba Bola Tinubu da tsohon minista, Uche Nnaji. Hoto: Bayo Onanuga, Uche Nnaji.
Source: Twitter

Hakan ya biyo bayan tuhumar ICPC bayan binciken shekaru biyu da Premium Times ta gudanar, wanda ya bayyana cewa ya gabatar da jabun takardun digiri da NYSC.

A watan Yunin 2026, majiyoyi sun ruwaito cewa ICPC na neman Nnaji bayan ya ki amsa gayyata da hukumar ta aika masa.

Uche Nnaji ya musanta zancen gayyatar ICPC

Duk da haka, Nnaji ya musanta rahotannin, yana cewa babu wata hukumar ICPC da ke nemansa, tare da zargin gwamnatin Enugu da yada ƙarya.

Sai dai takardun da aka samu sun nuna cewa ICPC ta aika masa wasiƙar gayyata mai ɗauke da kwanan watan 15 ga Mayu 2026.

A cikin wasiƙar, hukumar ta bukaci ya halarci zaman tambayoyi a hedikwatar ICPC da ke Abuja ranar 20 ga Mayu da ƙarfe 10:00 na safe.

Rahotanni sun nuna cewa an aika wasiƙar zuwa lambobin WhatsApp da adireshin imel ɗinsa, tare da saƙon tunatarwa kafin ranar.

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar jigo a Izala, tsohon shugaban APC ya rasu a hannun yan bindiga

Duk da haka, Nnaji bai halarci zaman tambayoyin ranar 20 ga Mayu ba, lamarin da ya sa hukumar ta sake tsara wata rana.

An sake ɗaga zaman zuwa ranar 3 ga Yuni 2026, tare da roƙonsa ya halarta domin tabbatar da adalci da ba shi damar kare kansa.

Sai dai ya sake ƙin bayyana a ranar da aka ɗaga zaman, abin da ya fusata jami’an hukumar binciken cin hanci.

Yadda ICPC ta tura gayyata ga tsohon minista amma ya ki zuwa
Tsohon minista a gwamnatin Bola Tinubu, Uche Nnaji. Hoto: Uche Nnaji.
Source: UGC

Zargin Nnaji da amfani da takardun bogi

Tun a shekarar 2023 ne aka ta fara binciken bayanan karatun Nnaji bayan ya gabatar da takardunsa wajen tantance ministoci.

Jami’ar Najeriya da ke Nsukka ta tabbatar cewa an taɓa ba shi gurbin karatu, amma bai kammala karatunsa ba kuma ba a ba shi takardar digiri ba.

Hukumar NYSC ma ta nesanta kanta daga takardar shaidar kammala hidima da tsohon ministan ke amfani da ita.

Bayan fallasa batun, Nnaji ya yi murabus daga mukaminsa, amma mutane da dama sun nemi a gurfanar da shi a gaban kotu.

Wani kwamitin bincike da Ma’aikatar Ilimi ta kafa ya kuma tabbatar cewa ya yi amfani da jabun takardun digiri da NYSC.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Gwamnatin Tinubu ta kawo shaidu 30 da za su ba da shaida a kotu

Kotu ta umarci kama tsohon minista

Mun ba ku labari a baya cewa rahotanni sun nuna cewa Babbar Kotun Tarayya ta umarci ICPC ta kama tsohon minista, Uche Nnaji kan zargin amfani da takardun bogi.

ICPC ta ce ya ki amsa gayyatar bincike kan zargin wanda hakan ya kai ga kotu ta ba da izinin ayyana Nnaji a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

Bayan murabus a gwamnatin Bola Tinubu, tsohon ministan ya koma jam'iyyar PDP kuma ya samu titikin jam'iyyar na takarar gwamna a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.