Hukumar Hisbah za ta kama masu rawar fadi ka mutu a Kano
Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta sanar da cewar jami’an ta za su fara kama duk mutumin da aka sama yana taka sabuwar rawar nan ta 'fadi ka mutu' wanda ke tashe a yanzu.
A ranar Talatar da ta gabata ne wani bidiyo ya fito inda aka nuno wasu 'yan mata sanye da hijabi na tikar rawar da ta samo asali daga kasar Afirka ta Kudu.
Wasu mutane sun ce 'yan matan da ke cikin bidiyon 'yan jihar Kano ne, amma kakakin hukumar Hisbah a Kano, Adamu Yahaya ya shaida wa majiyarmu ta BBC Hausa cewa ba su samu wani rahoto makamancin wannan ba.

Asali: UGC
Wannan sabuwar rawar ta samo asali ne daga wata waka da mawakin Afirka ta Kudu, King Monada, ya rera mai suna 'Maldwedhe' da aka ce tana caza kwakwalwar matasa.
KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta karyata batun hana shige da fice a Maiduguri
Ma'anar kalmar Maldwedhe ita ce cuta, kuma Monada ya yi amfani da kalmar ce dangane da wani maras lafiya da ke dauke da cutar wadda ke sa shi ya suma idan ya kama masoyiyarsa tare da wani.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng