El-Zakzaky: Yan Shi’a sun karyata Lai Mohammed kan cewa ana ciyar da shugabansu N3.5m duk wata

El-Zakzaky: Yan Shi’a sun karyata Lai Mohammed kan cewa ana ciyar da shugabansu N3.5m duk wata

Kungiyar yan uwa Musulmai na Shi’a sun bayyana cewa ikirarin da ministan labarai, Lai Mohammed ya yi cewa gwamnatin tarayya na kashe naira miliyan 3.5 duk wata wajen ciyar da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shugaban kungiyar da ke tsare bai nuna a jikinsa ba duba ga halin da yake ciki.

Shugaban kungiyar na ýan Shi’a, Ibrahim Musa ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a, 9 ga watan Nuwamba a Abuja.

Ya bayyana ikirarin Mohammed a matsayin makirci domin sakaya take hakkin Zakzaky da na mabiyansa da gwamnati ta yi.

El-Zakzaky: Yan Shi’a sun karyata Lai Mohammed kan cewa ana ciyar da shugabansu N3.5m duk wata

El-Zakzaky: Yan Shi’a sun karyata Lai Mohammed kan cewa ana ciyar da shugabansu N3.5m duk wata
Source: Facebook

Musa ya ci gaba da cewa yanayin ciyar da El-Zakzaky ya tabarbare tun bayan da aka mayar da shi Kaduna daga Abua tsawon watanni shida da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari, gwamnoni 3 da sauransu sun bar Abuja domin halartan taron kungiyar zaman lafiya a Faransa

Sannan ya bayar da shawarar sakin malamin maimakon kashe kudaden jama’a wajen ciyar da shi kamar yadda suka yi ikirari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel