Sauya shekar yan majalisa: APC na fafutukar ganin ta ci gaba da kasancewa mafi rinjaye
Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC sunyi gab da rasa matsayinsu na masu rinjaye a majalisar dokokin kasara a watan Yuli im kadan kafin majalisar dokokin ta fara hutun ta na shekara.
Da fari mambobin jam’iyyar 37 ne suka sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun siyasa, inda babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta yi nasarar cafke masu sauya sheka 32.
Hakan ya tayar da kura a tsakanin shugabannin jam’iyyar, wanda ya kai har said a suka rabe aka kafa kungiyar sabuwar APC.
Sakamakon haka, shugaban majalisam Femi Gbajabiamila yace masu ruwa da tsaki na APC za su shigar da wadanda suka sauya shekar kotu, inda ya kafa hujja da sashi 68(g) na kundin tsarin mulki, wanda ke nuni ga cewa dan majalisa na iya rasa kujerarsa a majalisar.

Asali: UGC
Sai dai APC na ta kokarin ganin ta rike matsayarta na masu rinjaye a majalisa, amma sai gashi an ci gaba da yiwa jam’iyyar dauki dai-dai.
Sai gashi kuma a yanzu mafi akasarin yan majalisar sun rasa tikitin dawowa majalisa inda hakan ya sake tayar da kura, duk da cewar jam’iyyar na ta kokarin ganin ta sasanta da fusatattun mambobin nata a majalsa.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Najerita ba ta zauna da Kungiyar ASUU ba har yanzu – Inji Ogunyemi
Bayan ganawa da suka yi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, fusatattun yan majalisan sun bukaci shugaban kasar da yayi amfani da karfin kujerarsa wajen magance lamain tun kafin lokaci ya kure.
Sai dai a yanzu ana ganin akwai aiki a ja a gaban jam’iyyar domin Soba wanda ake gani shine babban bango tsakanin masu fafutukar da shugaban kasa ya sauya sheka.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng