Karya kuke yi – Dan Fulani ga malaman da suka yi hasashen faduwar Buhari a 2019
Shugaban kungiyar magoya bayan shugaban kasa Buhari, wato Buhari Presidential Support Committee (BPSC), Alhaji Ya’u Adamu dan Fulani, ya yi watsi da hasashen wasu malaman Najeriya game da zaben 2019.
Sahara Reporters ta ruwaito cewa ya bayyana cewa ana kamfen din Buhari ne akan tarin nasara da ya samu ba wai akan shafawa juna bakin fenti ba.
Legit.ng ta tattaro cewa Dan Fulani ya bayyana cewa dukkanin rikice-rikice na addini siyasa ce kuma an shirya ta ne domin bata sunan gwamnatin Buhari.

Asali: Depositphotos
An tattaro cewa Boss Mustapha, babban saataren gwamnatin tarayya ne ya kafa kungiyar kwanakin baya.
Ya bayyana malaman da suka yi hasashen cewa Shugaba Buhari zai sha kaye a matsayin mabarata kuma makaryata da ke son samun kudi daga yan sisaya da ke da kudi.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta janye belin tsohon gwamnan Abia Orji Kalu kan rashin gurfana a gabanta
Dan Fulani ya bayyana cewa Buhari zai lallasa dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar a zaben 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng