An rufe makarantar sakandare ta jami’ar Ibadan saboda rigimar hijabi

An rufe makarantar sakandare ta jami’ar Ibadan saboda rigimar hijabi

Wani rigima ya kaure a makarantar sakandare mai zaman kanta ta Jami'ar Ibadan wato UI Intrnational akmakon kora dalibaida aka yi zuwa gidajensu.

Iyayen daliban sun zargi hukumar kula da harkokin makarantar da rufe makaranta sakamakon fara sanya hijabi da dalibai musulmai suka yi.

Sai dai kuma hukumar makarantar ta karyata zargin rufe makarantar, sai dai ta ce ta haramta a shiga da hijabi a matsayin inifam din makaranta.

An rufe makarantar sakandare ta jami’ar Ibadan saboda rigimar hijabi
An rufe makarantar sakandare ta jami’ar Ibadan saboda rigimar hijabi
Asali: UGC

Tuni dai kungiyar kare hakkokin musulmai ta Muslim Rights Concern ta yi Allah wadai da wannan mataki da shugabannin makarantar suka dauka.

KU KARANTA KUMA: APC da wasu jam’iyyu 7 sun hada karfi da karfe don yi ma PDP taron dangi a zaben jahar Kwara

Shugan makarantar a bayyana cewa a ranar Litinin ce wasu iyaye musulmi suka shigo makaranta suka raba hijabi ga dalibai - wani abu da ya saba da tsarin gudanawar makarantar.

Bincike ya tabbatar da cewa an kulle makarantar sai dai an bar makarantar a bude ga dalibai 'yan aji uku kadai da ke shirin rubuta jarrabawar karshe, inda rahotanni suka nuna sauran daliban an tasa keyarsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng