2019: Dan takarar kujeran dan majalisa na APC a Adamawa ya koma PDP

2019: Dan takarar kujeran dan majalisa na APC a Adamawa ya koma PDP

Wani dan takarar kujeran siyasa na APC a zaben fidda gwani da aka kammala a jihar Adamawa, Habila Istifanus ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, inda ya bayyana rashin adalci a zaben fidda gwani da aka kammala a matsayin dalilinsa na barin jam’iyya mai mulki.

Istifanus ya yi korafin cewa zaben fidda gwanin jam’iyyar a jihar ya kasance cike da rigingimu sannan cewa Gwamnan jihar Adamawa Mohammed Umaru Jibrilla wanda shine yayi sanadiyar shigarsa APC ya gaza cika kowani alkawari da ya daukar masa kafin komawarsa jam’iyyar.

Ya ce ya yanke shawarar komawa PDP ne domin ganin ya yiwa mutanensa aiki nagari.

2019: Dan takarar kujeran dan majalisa na APC a Adamawa ya koma PDP
2019: Dan takarar kujeran dan majalisa na APC a Adamawa ya koma PDP
Asali: Depositphotos

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 12 ga watan Nuwamba a garin Yola, babbar birnin jihar ta Adamawa.

KU KARANTA KUMA: Magu ya yi buris da tambaya akan bidiyon cin hanci na Ganduje

A wani lamari na daban, mun ji cewa Shugaban kungiyar magoya bayan shugaban kasa Buhari, wato Buhari Presidential Support Committee (BPSC), Alhaji Ya’u Adamu dan Fulani, ya yi watsi da hasashen wasu malaman Najeriya game da zaben 2019.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa ya bayyana cewa ana kamfen din Buhari ne akan tarin nasara da ya samu ba wai akan shafawa juna bakin fenti ba.

Legit.ng ta tattaro cewa Dan Fulani ya bayyana cewa dukkanin rikice-rikice na addini siyasa ce kuma an shirya ta ne domin bata sunan gwamnatin Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng