Burina ya cika da na tsinci kaina a Kannywood – Teema Yola

Burina ya cika da na tsinci kaina a Kannywood – Teema Yola

Shahararriyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa, Fatima Isa wacce aka fi sani da Teema Yola ta bayyana cewa babu wani tasiri da Fina-finan Indiyan Hausa zai yi kan na Kannywood duk da ko sun karade kasuwani.

Teema ta nuna farin ciki da cikar burinta wanda a cewarta tuna tana yar kamarta burinta shine ganin kanta a masana’antar shirya fina-finai, kuma gashi Allah ya cika mata wannan buri nata

Jarumar ta bayyana hakan ne a hira da tayi da Premium Times a jihar Kaduna.

Burina ya cika da na tsinci kaina a Kannywood – Teema Yola
Burina ya cika da na tsinci kaina a Kannywood – Teema Yola
Asali: UGC

Ta kuma bayyana cewa tun bayan fara bayyanarta a wasanni, bata taba yin koda musayar yawu ba da wata ba ko wani Forodusa, ko Darekta. Tace kowa takan dauke shi dan uwanta ne.

KU KARANTA KUMA: Kwamitin shgaban kasa ta yi barazanar kai mamaya gidan dan takara gwamna a APC

Da aka tambaye ta ko rashin fitowar fim a kasuwanni yanzu zai iya kawo wa masu shirya fim din wani matsala sai tace: ”Babu wani matsala da hakan zai yi. Sinima ake fara nunawa inda bayan an nuna a nan sai kuma a sake shi a kasuwa. Ni banga wani matsala da yake kawo wa ba.

”A harka ta babu matsala kuma ba zai shafi shanawar tauraro na ba.”

Bayan nan Teema ta yabi wasu daga cikin abokanan aikin ta kamar Fati Su, inda ta kurantata da cewa macece mai kamar maza.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel