Tsare ni da ake yi hauka ne da rashin hankali da Kuma cin zarafi - Zakzaky

Tsare ni da ake yi hauka ne da rashin hankali da Kuma cin zarafi - Zakzaky

A yau Laraba, 7 ga watan Nuwamba ne aka sake gurfanar da shugaban kungiyar yan Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky karo na biyu a gaban babbar kotun jihar Kaduna domin ci gaba da shari’ar da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar akan shi.

Bayan gabatarwa da lauyan gwamnati ya karanto dalilin zaman sai Alkali ya jero tuhume-tuhume da ake yiwa shugaban Yan Shi’an.

Amma ga dukkan alamu Zakzaky ya fusata bisa la’akari da irin amsar da ya bayar akan tuhumar da ake yi masa, inda ya bayyana cewa tuhumar da ake yi masa ba komai bane face hauka, rashin hankali, da kuma cin zarafi.

Tsare ni da ake yi hauka ne da rashin hankali da Kuma cin zarafi - Zakzaky
Tsare ni da ake yi hauka ne da rashin hankali da Kuma cin zarafi - Zakzaky
Asali: Facebook

Ya ce: “tuhumar da ake min haukane, rashin hankali ne kuma cin zarafi ne gareni”.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan bindiga sun kashe wani hamshakin mai kudi a Katsina

Bayan alkali ya karanto tuhume ta biyu ya maimaita cewa wannan itace amsar shi. Daga karshe alkalin kotun yasake dage shari'ar zuwa ranar 22 ga watan Janairun 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel