An Daga Shari'a, El Rufa'i zai Shafe kusan Kwana 100 a Rufe kafin a Dawo Kotu

An Daga Shari'a, El Rufa'i zai Shafe kusan Kwana 100 a Rufe kafin a Dawo Kotu

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya shafe sama da kwanaki 120 a tsare a hannun hukumomi tun 16 ga Fabrairun 2026
  • Yayin da tsohon gwamnan ke tsare, kotu ta ɗage shari’ar cewa El-Rufa'i ya saurari wayar Nuhu Ribadu zuwa ranar 22 ga Satumban 2026
  • Za a cigaba da rike shi saboda ya kasa cika sharudan beli da suka haɗa da samun ma'aikaci mai gida Maitama ko Asokoro a Abuja da zai tsaya masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shafe aƙalla kwanaki 126 a tsare bisa tuhume-tuhumen da suka haɗa da zargin amfani da mukami ba daidai ba da sauransu.

Ana cigaba da rike tsohon gwamnan ne sakamakon kasa cika sharudan beli da ake ganin suna da tsauri da kotuna daban-daban suka gindaya masa.

Kara karanta wannan

"Ba makamin azabatarwa ba ne"; Atiku ya nuna damuwa kan sharuddan belin El Rufai

Malam Nasiru El-Rufa'i
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa'i. Hoto: Bello El-Rufa'i
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa idan har ya ci gaba da kasancewa a tsare har zuwa ranar da aka ɗage shari’ar zuwa, wato 22 ga Satumba, 2026, zai kasance ya shafe kwanaki 217 a tsare.

An kama El-Rufa'i ne 16 ga Fabrairu, 2026, sai dai an taɓa sakin shi na tsawon kwanaki biyu domin halartar jana’izar mahaifiyarsa da ta rasu.

Yadda zaman kotu ya gudana

A zaman kotun da ya gudana a ranar Talata, DSS ta tabbatar da kammala gabatar da shaidunta bayan kiran shaidu biyu kacal.

Shaidun sun haɗa da wani jami’in DSS da ya ba da shaida a watan da ya gabata, da kuma lauya kuma ɗan gwagwarmaya, Deji Adeyanju, wanda ya bayar da shaida a ranar Litinin.

Lauyan masu gabatar da ƙara, Oluwole Aladedoye (SAN), ya sanar da kotu cewa sun kammala gabatar da dukkan shaidunsu.

Sai dai lauyan El-Rufai, Paul Erokoro (SAN), ya ce ɓangaren su zai gabatar da buƙatar cewa babu hujjojin da za su sa a ci gaba da shari’ar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi maganar da ta ba da mamaki kan tsaro

Ya nemi kotu ta ba shi makonni biyu domin gabatar da wannan buƙata, yayin da masu gabatar da ƙarar suka nemi lokaci makamancin haka domin mayar da martani.

Nasir El-Rufa'i a kotu
Jami'an tsaro da Nasir El-Rufa'i a kotu. Hoto: Uche Diala
Source: Facebook

An daga shari'ar Nasir El-Rufa'i

Bayan sauraren ɓangarorin biyu, mai shari’a Joyce Abdulmalik ta ƙi amincewa da buƙatar sassauta sharudan belin El-Rufa'i, tana mai cewa mai neman sassaucin bai gabatar da gamsassun dalilai ba.

Kotun ta kuma bayyana cewa akwai ma’aikatan gwamnati da suka mallaki kadarori a wuraren da aka nemi Nasir El-Rufa'i ya kawo.

Vanguard ta wallafa cewa kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 22 ga Satumba 2026 domin gabatar da buƙatar rashin hujjoji da kuma ci gaba da sauraron shari’ar, za a shafe kwana 92 kafin a dawo.

Muhammadu Sanusi II ya magantu kan El-Rufa'i

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan sharudan belin da aka sanya wa Nasiru El-Rufa'i.

Sarkin ya bayyana cewa an sanya masa sharuda masu tsauri wajen bayar da beli da ba a taba sanya wa wani mutum ba a kasar nan.

Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa rashin adalci ne babban abin da ya ke hana Najeriya cigaba da magance matsalolinta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng