Shettima, Gwamnoni, Malamai, Sarakuna Sun Hallara Taron Tuna Mamar Tinubu

Shettima, Gwamnoni, Malamai, Sarakuna Sun Hallara Taron Tuna Mamar Tinubu

  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya yaba da halin mahaifiyar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Hajiya Abibatu Mogaji
  • Da ya ke bayani a wajen taron addu'o'i da tunawa da ita, Shettima ya ce har yanzu dattakunta na tasiri a Najeriya lura da abin da danta ke yi
  • Hadimin shugaban kasa, Ibrahim Kabir Masari ya sanar da cewa an yi rijiyoyin burtsatse sama da 200 a wasu jihohin Arewa domin tunawa da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya yaba wa mahaifiyar shugaba Bola Ahmed Tinubu, marigayiya Abibatu Mogaji.

Ya bayyana ta a matsayin shugaba mai sadaukar da kai kuma har yanzu tana ci gaba da tasiri a Najeriya ta hanyar dabi'u da ta dasa a ɗanta.

Kara karanta wannan

'Za ta karewa Tinubu a 2027,' Momodu ya fadi yadda Atiku zai kifar da APC

Shettima a taron tunawa da mamar Tinubu
Kashim Shettima da manyan kasa wajen taron tunawa da mamar Bola Tinubu. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Kashim Shettima ya wallafa hotunan da suka dauka a wajen da aka yi wa marigayiyar addu'o'i a Abuja domin tunawa da ita a Facebook.

Maganar da Shettima ya yi

Da yake jawabi a wajen taron addu'o'in, Shettima ya ce marigayiyar ta kasance abin koyi a bangaren shugabanci wajen kawo sauyi a rayuwar jama'a.

Rahotan the Guardian ya nuna cewa Hajiya Abibatu Mogaji ta rasu a ranar 15 ga Yuni, 2013, tana da shekara 96 a duniya.

Shettima ya ce jajircewar shugaba Tinubu wajen hidimar jama'a da manufofin dimokuraɗiyya ta samo asali ne daga ƙa'idojin da mahaifiyarsa ta koya masa.

“Ba abin mamaki ba ne cewa ɗan da ta raina ya kai zuwa ofishi mafi girma a ƙasarmu,”

In ji shi.

Ya yi addu'ar Allah Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya ba ta madawwamin hutu a aljanna, sannan Ya bai wa shugaba Tinubu da daukacin iyalansu juriyar rashin.

Kara karanta wannan

Sojoji za su fara shiga daji yaki da 'yan bindiga tare da 'yan jarida

Taron tunawa da mamar Tinubu a Abuja
Mahalarta taron addu'o'i ga mamar Bola Tinubu a Abuja. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Bayanin wanda ya shirya taron

Hadimin Tinubu da ya shirya taron, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ya bayyana Hajiya Abibatu Mogaji a matsayin mace wadda rayuwarta ta kasance cike da hidima da tausayi.

Masari ya bayyana cewa an gina rijiyoyin burtsatse sama da 250 a jihohi tara na Arewa domin tunawa da ita, lamarin da ya samar da tsaftataccen ruwa ga dubban mazauna yankunan.

Ya kuma sanar da shirin kafa cibiyar Musulunci ta Abibatu Mogaji a Abuja domin bunƙasa ilimi, tare da gina babban masallacin Juma'a a Rigasa, jihar Kaduna, domin girmama ta.

Gwamnoni da Kashim Shettima
Kashim Shettima da wasu gwamnoni bayan taron addu'a ga mamar Tinubu. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Wanda suka je taron mamar Tinubu

Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai gwamnonin jihohin Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum; Yobe, Mai Mala Buni; da Jigawa, Umar Namadi.

Tsofaffin gwamnoni Usman Sa’idu Nasamu Dakingari da Tanko Al-Makura; Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, wanda Yahaya Abubakar ya wakilta duk sun hallara.

Kara karanta wannan

An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya

Ministan gidaje, Dr Muttaqha Rabe Darma; ministan kasafi, Abubakar Atiku Bagudu; shugaban NCAOOSCE, Dr Mohammed Sani Idris, tare da manyan jami'an gwamnati, sarakunan gargajiya da shugabannin addini sun je taron.

Ana batun Tinubu ya yi murabus

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu 'yan majalisar wakilai da suka fito daga jam'iyyun adawa sun fara kira ga shugaban kasa Bola Tinubu ya yi murabus.

A wani taron manema labarai da suka shirya, 'yan majalisar sun bayyana cewa sun yi kiran ne saboda yadda lamuran tsaro suka lalace a kasar nan.

Sai dai jam'iyyar APC mai mulki ta yi tir da batun, tana mai cewa shugaba Bola Tinubu na matukar kokari wajen shawo kan matsalolin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng